Sabira Mukhtar
Sabira Mukhtar
Jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato kannywood tana daya daga cikin kyawawan mata a masana'antar. Ta kuma fito a fim din FANAN [1]Wanda ya Kara haskakata a masana'antar ya Kuma fito da ita a idon duniya jarumar ta sami kyaututtukan da lambar girmamawa da yabo[2]
Takaitaccen Tarihin Ta
[gyara sashe | gyara masomin]sabira mukhtar wacce aka Fi sani da sabeerah ko Kuma sabby baby, jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa, an haifeta a ranar 16 ga watan disamba . Tana zaune a cikin garin Kano tare da mahaifiyar ta, mahaifin ta ya rasu . Ta shigo masana'antar fim a shekarar 2014 inda ta fito a Farkon fim din ta Mai suna KUSUFI , fim din ta na biyu shine MATAR MAHAUKACI Wanda sukayi da sarki Ali nuhu Wanda darakta Ali gumzak ya Bada umarni. Bayan tayi shekaru biyu a masana'antar tai aure inda ta auri Wani Dan kasuwa a shekarar 2016, auren be Dade ba suka rabu da mijin inda tayi wasu shekaru ba,a ganta a fim ba daga baya ta dawo. Ta dawo masana'antar fim a shekarar 2018 inda ta dawo tana Hawa Wakokin soyayyah ta Hau wakar salon so da misbahu AkA anfara, ta Kuma Hau Waka da jarumi Adamu zango Mai suna Yanayin rayuwa.daga Nan ta fito a fina finan da dama kamar su.
- shimfidar fuska
- Tsalle daya
- Bazan haihu ba
- Fanan[3]
- ↑ https://fimmagazine.com/tag/sabira-mukhtar/
- ↑ https://manhaja.blueprint.ng/fim-%C9%97in-fanan-ya-fito-da-ni-idon-duniya-jaruma-sabira-mukhtar/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-29. Retrieved 2023-07-29.