Jump to content

Sadiya kabala

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sadiya_Kabala

Sadiya Kabala na daya daga cikin fitattu kuma kyawawa a masana'antar Kannywood dake da reshe a jahar Kano. Sadiya Kabala fitacciyar jarumar Kannywood ce dakeda dunbin masoya maza da mata. Jarumar Sadiya ana kiranta da sadiya skl, an haifi fitacciyar jarumar a ranar 27 ga watan june,shekara ta 1992 a jahar kadunan Najeriya. Inda ta gorma a jihar Kaduna tare da iyayenta.

Sadiya kabala ta kammala karatunta na firamare da sakandare a jihar kaduna, a yanzu haka Jaruma kabala na zaune ne a jahar Kano

Jaruma kabala ta taba lashe  kyauta a matsayin City Entertainment People Award na shekarar 2016, kuma ta fitowa a fina-finai da dama kamar korarriya, Amaryan Kauye, Kwadayi Da Buri, Makobcina, da sauransu.Jaruma kabala ta taba lashe kyauta a matsayin City Entertainment People Award na shekarar 2016, kuma ta fitowa a fina-finai da dama kamar korarriya, Amaryan Kauye, Kwadayi Da Buri, Makobcina, da sauransu.