Sai'du Ahmed Alkali

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sa'idu Ahmed Alkali (An haifi shi a ranar 12 ga watan Fabrairu, shekara ta 1969). Ya rike sarautar Sarkin Gabas na Dukku. ya samu digirin farko na Kimiyya a fannin tattalin arziki, kuma ya zama ma'aikacin gwamnati.[1] kuma ya taɓa zama kwamishinan yaɗa labarai a gwamnatin Gwamna Danjuma Goje .[2]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan rasuwar Kawu Peto Dukku a watan Afrilu shekara ta 2010, ya fito a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP musamman saboda ya fito daga karamar hukumar Dukku. Wannan shawarar da aka yi a kan yanayin kasa ta samu suka daga wasu ‘yan jam’iyyar.[3] A zaben tarayya na watan Afrilun shekara ta 2011. Alkali yayi nasara, inda ya samu kuri’u 136,850 a jam’iyyar PDP. Mu'azu Umar Babagoro na jam'iyyar CPC ya samu kuri'u 81,519 sai, kuma Injiniya Abdullahi Sa'ad Abubakar na jam'iyyar All Nigeria People's Party, (ANPP)

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]