Saint Javelin

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Saint Javelin
Rayuwa
Sana'a

Saint Javelin wani dan hoton meme ne na Intanet wanda aka nuna a cikin sifar addini na wani mutum mai kama da waliyyai wanda ke ɗaure da wani makami na zamani wanda Rasha tayi amfani dashi wajen mamaye Yukren. Christian Borys ne ya kirkiri wannan dan meme din a yayin da Rasha ta farmaki kasar Ukraine a shekara ta 2022, kuma ya shahara a duniya, wanda ya haifar da wasu ire-iren memes din. Meme ɗin ya karawa mutane karfin gwiwa kuma an yi amfani da shi a samfuran kayayyaki, wanda ya haifar da tara kudi sama da dala miliyan ɗaya don kai agaji ga kasar Yukren.[1][2]

Bayani[gyara sashe | gyara masomin]

Wani dan jarida dan kasar Ukraine da Kanada Christian Borys ne ya kirkiro wannan tambarin, da farko don amfani dasu a matsayin tambari wadanda za a ba da kudaden da aka samu ga ayyukan jin kai a Ukraine.[3][4][5] meme din Saint Javelin ya mamaye yanar gizo a matsayin alamar juriya ga mamayewar Rasha na Ukraine.[6]

Christian Borys a halin yanzu yana zaune a Toronto amma a baya yana aiki a Ukraine a matsayin ɗan jarida a lokacin rikicin farko a 2014.[7] Yayin da yake wurin, ya kasance mai rubuce-rubuce ga ƙasashe daban-daban kuma ya damu sosai da halin marayu da zawarawa daga Yaƙin Donbas.[8]

Kamfe[gyara sashe | gyara masomin]

A baya Christian Borys ya yi aiki tare da wata kungiyar agaji ta Ukraine mai suna Help Us Help kuma ya ba da gudummawar kudaden farko daga sitikun Saint Javelin da aka sayar ta kafafen yanar gizo don taimakawa yara da marayu da yakin ya shafa.[9][6] Tun daga watan Maris 2022, Borys ya bayyana cewa yana shirin mmayar da tambarin 'Saint Javelin' don zama cikakken yunkuri kuma yana fatan ɗaukar ma'aikata na dindindin don ci gaba da tallafawa ƙoƙarin sake gina al'ummu bayan yaƙin ya ƙare.[10] Don taimakawa wajen sake gina Ukraine kai tsaye Borys ya yi ƙoƙarin samun ƙarin kayyaykin Saint Javelin da akayi a Ukraine don sayarwa da kuma samar da ayyukan yi ga mutanen Ukraine da kuma tara kuɗi daga ribar da za ta taimaka wajen sake gina Ukraine.[11]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Why - Let's Help Ukraine". Saint Javelin. Retrieved 2022-09-08.
  2. "How the St. Javelin meme raised a million dollars for Ukraine". Washington Post. ISSN 0190-8286. Retrieved 2022-09-19.
  3. "About Us". Saint Javelin. Retrieved 2022-09-08.
  4. "Sur les réseaux sociaux, mèmes et légendes se multiplient en soutien à l'Ukraine". L'Éclaireur Fnac (in French). 2022-03-07. Retrieved 2022-05-04.
  5. "Sur les réseaux sociaux, mèmes et légendes se multiplient en soutien à l'Ukraine". L'Éclaireur Fnac (in French). 2022-03-07. Retrieved 2022-05-04.
  6. 6.0 6.1 Dart, Chris (March 2, 2022). "How a Canadian artist is using the Saint Javelin meme to raise money for Ukraine". Canadian Broadcasting Corporation.
  7. Dart, Chris (March 2, 2022). "How a Canadian artist is using the Saint Javelin meme to raise money for Ukraine". Canadian Broadcasting Corporation.
  8. "How 'Saint Javelin' raised over $1m for Ukraine". BBC News. 2022-03-10. Retrieved 2022-05-04.
  9. "Why - Let's Help Ukraine". Saint Javelin. Retrieved 2022-09-08.
  10. "How 'Saint Javelin' raised over $1m for Ukraine". BBC News. 2022-03-10. Retrieved 2022-09-08.
  11. "'Saint Javelin' viral meme turned into war merchandise, helps fund Ukrainian struggle | Watch News Videos Online". Global News. Retrieved 2022-09-08.