Sale Ahmad Marke
Appearance
Sale Ahmad Marke | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Dawakin Tofa, 26 ga Janairu, 1963 (61 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Sale Ahmad Marke (26 ga Janairu, 1963) a ƙauyen Dambaje na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa. Ya fito daga unguwar Marke. [1]
Karatu da Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Ya halarci Makarantar Firamare ta Marke (1970 – 1977) da Makarantar Sakandare ta Garko, 1977 – 1982. Honorabul Marke ya taɓa zama Malamin Makarantar Firamare, Malamin Kiwon Lafiyar Ƙaramar Hukumar kafin shiga siyasa. Daga shekarun 1999 – 2003, an zaɓe shi kansila. [2]
An fara zaɓen Honourable Marke a matsayin ɗan majalissar jiha a shekarar 2007 – 2011. An sake zaɓen shi a 2011 – 2015 da 2015 – 2019 bi da bi. kuma yanzu haka shine Shugaban Kwamitin Aikin Hajji Na jahar kano.