Jump to content

Salihu Jankiɗi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Salihu Jan kiɗi)
Salihu Jankiɗi
Rayuwa
Haihuwa 1853
ƙasa Daular Sokoto
Mallakar Najeriya
Najeriya
Mutuwa 1973
Sana'a
Sana'a maiwaƙe da mawaƙi
Salihu

Salihu Alhasan Jankidi, Yana ɗaya daga cikin fitattun mawakan kasar hausa. An haifi Salihu Jankiɗi ne a garin Rawayya ta ƙasar Bunguɗu ne a yanzu cikin karamar Hukumar Gusau, wajajen shekarar alif ta 1852 zuwa shekara ta alif 1853[1]. Sunan mahaifinsa Alhassan ɗan Giye Ɗan Tigari mai abin kiɗi. Salihu shi ne sunansa na yanka, amma ƙannen uwarsa Karɓau ya yi masa laƙabi na Jankiɗi saboda jan da Allah ya ba shi wanda ya bi shi har bayan rasuwarsa.

Alhassan Giye Dan Tigari

Mahaifin Jankiɗi Alhassan Makaɗi ne na kalangu kuma mai yawan yawace-yawace don kiɗa. Yakan bar garinsu Rawayya ya shiga uwa duniya don sana’arsa ta kiɗa. Shi kuma makaɗi ne na lokacin kiɗan yaƙi. Ya je Argungu da Bida da Kwantagora da Kotonkoro da sauransu, amma yana komawa gida Rawayya. Daga baya ya tashi zuwa Kotonkoro, sai kuma ya tare Kwantagora wurin sarkin Sudan Ibrahim. Kuruciyarsa da tasowarsa

Salihu Jankiɗi ya buɗe idonsa a Kwantagora a nan ne ya yi rayuwarsa ta ƙuruciya. Ya tashi yana yaro mai ƙarfi da kurari, da ƙwarjini a tsakanin jama’a, sannan ja ne kamar tsada, tsaka-tsaki ne a wajen ƙirar jikinsa dangane da tsawo da gaba. Jankiɗi ya yi dambe da kokawa da sauran wasu ayyukan samartaka na sha’awa. Saboda kasancewar Salihu ya tashi cikin yaƙe-yaƙe kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka duk kusan abubuwan da ya yi na yarinta na nuna ƙarfi da bajinta ne. Ya yi karatun allo inda har ya sauƙe Alƙur’ani mai tsarki ya kuma karanta wasu daga cikin ƙananan littattafan addinin Musulunci kamar Ƙawa’idi da Ishmawi da Kurɗabi da sauransu. Amma fa bai yi ilimin addini na littattafai mai zurfi ba.

Koyo da fara waƙoƙinsa

[gyara sashe | gyara masomin]

Makaɗi Alhassan shi ne ya fara koya masa kiɗa da waƙa inda ya soma bin sa kiɗa har ya fara kaɗa kuntakuru watau kanzagi. Daga nan kuma ya shiga cikin yayensa mata masu amshi. Lokacin masu yi wa mahaifin nasa amshi, su ne:

  • Umma Tsohuwa
  • A’ishatu
  • Halimatu Bakabai

Salihu Jankiɗi — daga baya ya soma. Haka kuma mahaifinsa Alhassan ya taɓa ba da shi riƙo ga ɗan’uwansa makaɗa Ɗan Yawuri don ya koyi kiɗan kalangu sosai da sosai,

Bayan rasuwar Alhassan, sai Salihu Jankiɗi ya ɗauki shugabancin kiɗa a nan Kwantagora tare da waɗannan mataimaka:

  • Alhajiya — ‘Yar Halimatu Bakaba
  • A’ishatu
  • Halimatu Bakaba

Koyo da fara waƙoƙinsa

[gyara sashe | gyara masomin]

A lokacin da ya fara kiɗan, sai ya haɗa kiɗan noma da kiɗan fawa a lokaci guda yana ta yi duk wanda ya samu a yi. Kuma da dai kalangu gadon gidansu yake wannan nau’in kiɗa. Daga cikin yaƙi da ya yi na farko-farko, akwai wannan:

Yo gaba dai salsalon niƙatau,
Sanda mazan burdumi da galma.
Mai son noma da ɗan magaji,
Sai shi biɗo sulkuna da gari,
Don a yi kwanan wata gudane

Bayan da Turawan mulkin mallaka suka fara yaƙe-yaƙensu da ƙasashen Hausa har lokacin da suka zo ita Kwantagora suka yi yaƙi da ita, sai Kwantagora ta fashe. A wannan halin ne Salihu Jankiɗi da sauran iyalinsa suka koma Kotonkoro. Daga nan sai Bagega cikin ƙasar Talatar Mafara, sai zuwa Kanoma, sai Bunguɗu, sai ya sake komawa Kwantagora bayan ƙare yaƙi.

Daga nan kuma sai Salihu Jankiɗi ya koma gida Rawayya. Da yaƙi da Turawa ya ƙare, watau sun kama dukkan ƙasashen Nijeriya sosai, suka kuma shimfiɗa mulki irin nasu wanda suke buƙata, sai sarakunan da Turawan suka tabbatar (sababbi da tsoffafi) suka ci gaba da mulkin ƙasashensu. Daga wannan lokaci ne fa Salihu ya Jefar da kalangu ya kama taushi a shekara ta (tafashe) gadan-gadan yana yi wa sarakuna waƙoƙi. To, sai daga Rawayya ya koma Tsahe wurin ‘Yandoto Muhammadu a shekara (1897—1924) da ‘Yandoto Ibrahim Maikano a shekara ta (1926—1928) ya yi musu waƙoƙi. Sai kuma Salihu Jankiɗi ya kwashe iyalinsa ya koma Gusau da zama wajen sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Mai’akwai shekara ta (1929—1943). Daga Gusau Salihu Jankiɗi bai koma cirawa zuwa wani wuri da nufm ya zauna ba, sai dai ya je ya kai kiɗa ya dawo Gusau ɗin. A cikin wata waƙa da ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Mai’akwai yana cewa:

Ni Jankiɗi ba ni zuwa ko’ina,
Kwaɗai na ba shi wucewar Gusau.
Lalle ba mu zuwa ko’ina
Kwaɗai na ba shi zuwa ko’ina.

Bayan da aka fitar da sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Mai akwai aka naɗa Shehu ɗan Sama’iIa sarkin Kudu (1943—1945), sai Jankiɗi ya koma wurin Sarkin Musulmi Abubakar III shekara ta (1938—1988) ya zama ubangidansa. suna zaune tare da sarkin Musulmi har zuwa lokacin da ya naɗa shi sarkin taushinsa. A wajen naɗin nasa an yi gagarumin buki inda makaɗa yan’uwansa suka haɗu, aka yi masa tattaki, magaji mai farai shi ne ma ya yi busar naɗin don sheda wa jama’a.

A cikin wata waƙa da ya yi wa sarkin Musulmi, Salihu Jankiɗi ya yi godiya ainun. Yana cewa:

Godiya mu kai wa sarkin Musulmi,
Da yai ma sarkin taushi,
Yau batun Allah ya tabbata,
Babu sauran mai wata gardama.

(Jankiɗi: riƙa girma ka isa Bubakar)

Yaran Salihu Jankiɗi (‘Yan karɓi)

[gyara sashe | gyara masomin]

‘Yan karɓin Jankiɗi na farko na lokacin kiɗin noma da fawa da na samartaka su ne:

Aishatu Halimatu Bakaba Muhammadu Alhajiya Bahago Ajiya Yan karɓin Jankiɗi na faɗa

Makaɗa Ibrahim Ɗankaro ɗansa ne Mal. Abdullahi shi ma ɗansa ne. Musa Dangaladirna Labbo: ɗansa ne. MuhammaduTambai: Yaronsa ne. Hassan : ɗansa ne, Abduhlahi Jan Darno (Kaka): Yaronsa ne Na Goje : Yaronsa ne Umaru Ƙwairo : Yaronsa ne Yawace-yawacensa

Salihu Jankiɗi ya yawata mafi yawan ƙasashen Nijeriya, musamman ɓangaren Arewa. Ya zagaya dukkan manyan garuruwan jihar Sakkwato da wasu ƙananan garuruwan. Haka kuma ya je Kano da Haɗejiya da Daura da Katsina da Mani da Zariya da Kaduna da Bida da Ilorin da Minna da Ibadan da Lagos da Inugu kai da dai sauran ƙasashe.

Shirya waƙa

[gyara sashe | gyara masomin]

Da farko Sahihu Jankiɗi yakan sami labarai da bayanan da yake sa wa a waƙa ta hanyar fadawan sarki da hira da sarakuna kansu da ta ɓangaren hakimai da masu unguwanni. Kuma yana sane da abubuwan da yake gani suna gudana a fada da kuma cikin gari.

Salihu Jankiɗi mafi yawa ya fi tsayawa gida ya shirya waƙoƙinsa, kodayake yakan yi wasu waƙoƙin nan take inda duk suka samu. Amma waƙar da ya tsaya gida ya tsara ita ta fi daɗi da ƙayatarwa da ƙunsar abubuwan ban sha’awa.

Salihu Jankiɗi ya rasu ranar Juma’a 13 ga watan Oktoba shekara ta 1973 a lokacin yana da shekaru ɗari da ishirin (120) a duniya. Allah ya gafarta masa, yasa yahuta Aamiin.

  1. (Turanci) Graham Furniss, Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa, Edinburgh University Press for the International African Institute, 1996, p. 180.