Jump to content

Salimata Fofana

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Salimata Fofana
Rayuwa
Haihuwa 17 ga Augusta, 1997 (27 shekaru)
ƙasa Ivory Coast
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a judoka (en) Fassara

Salimata Fofana 'yar wasan judoka ce ta kasar Ivory Coast.[1] Ta lashe daya daga cikin lambobin tagulla a gasar mata mai nauyin kilogiram 52 a gasar Afrika ta shekarar 2015 da aka gudanar a Brazzaville na Jamhuriyar Congo.

Ta ci daya daga cikin lambobin tagulla a gasar mata mai nauyin kilo 52 a gasar Judo ta Afirka ta shekarar 2016 da aka gudanar a Tunis na kasar Tunisia da kuma gasar Judo ta Afirka ta shekarar 2019 da aka gudanar a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.

A cikin shekarar 2020, ta kuma lashe lambar tagulla a gasar mata mai nauyin kilo 52 a gasar Judo ta Afirka ta shekarar 2020 da aka gudanar a Antananarivo, Madagascar.[2] [3] A gasar Judo ta Afirka ta shekarar 2021 da aka yi a birnin Dakar na kasar Senegal, ta samu lambar azurfa a gasar.[4]

  1. "Salimata Fofana" . International Judo Federation. Retrieved 18 August 2021.
  2. Pavitt, Michael (17 December 2020). "Whitebooi retains title as African Judo Championships begins in Madagascar" . InsideTheGames.biz . Retrieved 5 July 2021.
  3. "2020 African Judo Championships" . African Judo Union . Archived from the original on 26 December 2020. Retrieved 26 December 2020.
  4. Rowbottom, Mike (21 May 2021). "Giantkiller Samy falls in final at 2021 African Judo Championships in Dakar" . InsideTheGames.biz . Retrieved 21 May 2021.