Saltcellar with Portuguese Figures
Saltcellar with Portuguese Figures | |
---|---|
Saltcellar with Portuguese Figures wani ma'ajin gishiri ne da ake sassaƙawa daga hauren giwa, wanda akayi a daular Benin dake afirka ta yamma a ƙarni na sha shidda da ake ƙera ma kasuwar Turawa. Ana danganta shi ga wani babban malami ko bita wanda ba a san shi ba wanda masana tarihi na fasaha suke kiranshi da Jagoran Heraldic Ship. Yana nuna wasu fitattun 'yan Portugal guda huɗu, biyu na manyan aji kuma sauran biyun wataƙila masu gadi ne da ke kare su. A cikin karni na 16. Maziyartan ƙasar Portugal sun b bada sautin mazubban gishiri na hauren giwa tare da maɗibansu masu irin abin nan. Wannan rumbun gishirin giwaye na Afro-Portuguese an sassaƙa shi da salon hauren giwar Benin, kwatankwacin shahararrun Tagullan Benin da kuma abin rufe fuska da akeyi dahga hauren giwa na Benin.[1]