Jump to content

Samfuri:Muƙalar mu a yau 02

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hijirar Sahabban Annabi Muhammad S.A.W zuwa Garin madina. A Lokacin da qurqishawa suka samu labarin yaɗuwan musulunci a cikin garin madina [yathrib] sai suka tsananta cutarwa ga sahabban Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi. Sai Manzon Allah ya umurce su da suyi hijira zuwa madina domin su haɗu da ƴenuwansu musulmai na garin madina [ANSAR]. Sai suka fara barin garin makka a ɓoye, saboda kada ƙuraishawa su hana su yin hijiran. A Lokacin sayyidina Abubakar yaso yayi hijira, sai Annabi ya hana shi, sai ya zauna tare da ANNABI a garin makka.

REFERENCE:KHULASATUN NURIL YAƘIN SHAFI NA 38