Samoëla
Samoëla Rasolofoniaina, wanda akafi sani da Samoëla, mawallafin murya ne dan ƙabilar Malagasy kuma mai ƙirƙirar folk fusion da tushen ƙiɗa na zamani dake janyo hankali akan ƙiɗe-ƙiɗe na gargajiya a ko ina a faɗin ƙasar Madagascar. Yawanci yana rera waƙa kuma yana kaɗa jita tare da gungu gami da jitar bass, Kawar turawan yamma da na gargajiya, da mawakan madadin. An bambanta shi ta hanyar yin amfani da waƙoƙin gargajiya na hainteny da yaren misalansa, da kuma zage-zage na matasa da harshe kai tsaye na ɓarna da al'adu don suka da kuma magance batutuwa masu mahimmanci na zamantakewa da siyasa.
TARIHIN RAYUWA
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Samoëla Rasolofoniaina a ranar 2 ga watan Afrilu ta shekarar alif dubu ɗaya da saba'in da da shidda. [1] A makaranta ya fara rubuta wakoki musamman irin salon wakokin Malagasy na gargajiya da ake kira hainteny, wanda ya ƙunshi karin magana da harshe na alama don magance batutuwa masu mahimmanci na al'ada. [2]