Samuel Kweku Obodai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Samuel Kweku Obodai
Member of the 5th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2009 - 6 ga Janairu, 2013
District: Agona West Constituency (en) Fassara
Election: 2008 Ghanaian general election (en) Fassara
Member of the 4th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2005 - 6 ga Janairu, 2009
District: Agona West Constituency (en) Fassara
Election: 2004 Ghanaian general election (en) Fassara
Member of the 3rd Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2001 - 6 ga Janairu, 2005
District: Agona West Constituency (en) Fassara
Election: 2000 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Agona District (en) Fassara, 29 ga Afirilu, 1960 (63 shekaru)
Karatu
Makaranta University of Cape Coast Digiri a kimiyya, diploma (en) Fassara, Master of Arts (en) Fassara : kimiya, Karantarwa, Mulki
Sana'a
Sana'a chemist (en) Fassara da ɗan siyasa
Imani
Addini Pentecostalism (en) Fassara
Jam'iyar siyasa New Patriotic Party

Samuel Obodai masanin sunadarai, mai ilmin a fannin kemistri ne kuma ɗan siyasar Ghana. Ya kasance ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Agona ta yamma a majalisa ta 5 a jamhuriya ta 4 ta Ghana.[1][2]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Obodai a ranar 29 ga watan Afrilu 1960. Garin sa shine Agona Nyakrom a yankin tsakiyar ƙasar Ghana. Ya kammala karatunsa na digiri na farko a fannin kimiyyar sinadarai da difloma a fannin ilimi daga Jami'ar Cape Coast a shekarar 1987. A cikin shekarar 2008, ya sami digiri na biyu na Arts a cikin Gudanar da Mulki da Jagoranci kuma daga Jami'ar Cape Coast.[1][2]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Obodai masanin kimiyya ne ta sana'a. Ya yi aiki tare da Major & Co Manufacturing Company Limited.[1][2]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya wakilci mazaɓar Agona ta yamma a matsayin ɗan majalisa a majalisa ta biyar a jamhuriya ta huɗu ta Ghana.[1][3][2] A shekara ta 2000, an zaɓi Mista Obodai wanda ya tsaya takarar babban zaɓen Ghana da Samuel Oppong na National Democratic Congress, Kojo Anan na National Reform Party, Mathew Caurie na jam'iyyar Convention People's Party, Abu Hamid Wanzam na People's National Convention da Joseph Archibald Ankrah wanda kuma ya tsaya takarar a People's National Convention. Samuel ya samu nasara ne da kuri'u 21,233 wanda yayi daidai da kashi 57.50 na kuri'un. Ɗan takarar majalisar dokokin NDC ya samu kuri'u 13,784 wanda ke wakiltar kashi 36.90%. Anan ya samu kuri'u 988 wanda shine kashi 2.60%. Mathew Caurie ya zo na 4 da kuri'u 679 wanda yayi daidai da kashi 1.80%. 'Yan takarar majalisar dokokin PNC guda biyu Wanzam da Ankrah sun samu kuri'u 430 wanda ya kai kashi 1.20% da kuri'u 0.[4] Ko da yake Obodai na fatan komawa majalisar, an kai karar kwamitin tantancewar jam’iyyar NPP da ta soke shi. Mai shigar da kara Samuel Krankye ya bayyana a wata wasika da ya aike wa kwamitin cewa Obodai bai bayar da gudumawa ba a kowane shiri na jam’iyyar.[5]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Obodai yana da aure da ‘ya’ya huɗu. Shi Kirista ne kuma yana bauta a Cocin Fentikos.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 "Ghana MPs - MP Details - Asare Kofi (Dr.)". www.ghanamps.com. Retrieved 2020-07-06.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 "Petitioner wants former MP Kweku Obodai disqualified". www.ghanaweb.com (in Turanci). 2020-03-02. Retrieved 2020-07-06.
  3. "Results Parliamentary Elections". www.ghanaweb.com. Retrieved 2020-07-06.
  4. "Parliament: Central Region". Peace FM Online. Retrieved 2020-09-06.
  5. "Petitioner wants Former MP Kweku Obodai disqualified". GhanaWeb. 2020-03-02. Retrieved 2020-09-06.