Sani Abubakar Lugga
Ka duba wannan shafin domin sanin yanda zaka gyara wannan mukalar Koyon rubuta mukala
Akwai yuwar admin ya goge wannan shafin matukar ba'a inganta ta ba. |
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Wazirin Katsina, Professor Sani Abubakar lugga an haife shi a ranar 28 ga watan Augusta a shekara ta 1950 a grin katsina, Jahar katsina dake Arewacin Najeriya. Da ne ga Alhaji Abubakar lugga ya rayu a shekarar (1912-1988) shine Sarkin Dawan katsina, wato mai kula da Dazuka da Ma'adanai na Masarautar katsina, Sarkin Dawan Katsina Alhaji Abubakar Lugga shine da na farko ga Wazirin Katsina Sheikh Haruna ya rayu a shekera (1857-1937) Don haka Wazirin katsina Prof. Sani Abubakar Lugga jika ne ga Wazirin Katsina na farko Sheikh Haruna. A tasawowar Prof. Sani Abubakar Lugga an kai Shi yaye wurin 'yar uwar kakarshi wadda takansance mai sani game da ilimin addinin Islama ana kiranta da Malama Aisha Sodai. Prof Sani an dauke shi an maida shi wurin iyayensa yana da shekaru bakwai 7 bayan yayi karatu na wajibi na Al-qur'ani, sai mahaifinsa ya sa shi a makarantar Firamare, amma ya cigaba da karatun Addini hade da karatun boko . Mahaifin sa Alhaji Abubakar lugga da ne ga Wazirin Katsina na farko Sheikh Haruna (1857-1937) wanda jika ne ga Sarkin Kanem Bakashe Mallam Haido (1899-1919) da ga Sarki Son Allah (1854-1882) Dan Sarki Iro (1824-1830), Dan Sarki Alu (1819-1822) Dan Sarki Ali (1802-1807) Dan Sarki E-E (1758-1779), Dan Sarki Remi (1744-1758), Dan Sarki Namauli 1706-1718), Dan Sarki Salifu (1661-1679), Dan Sarki Damisa (1634-1661), Dan Sarki Tanni (1579-1605), Wanda shine ya kafa daular Kanuri (Bare-Bari) masu mulki a Kanem Bakashe, Iyalan Sheikh Haruna asalinsu tsatso ne Kanuri wanda suke mulkin kanem Bakashe tun 1579 AD. Suna daga cikin wadanda suka kirkiri Daular Kanuri na Kanem Barno karkashin Mai Idris Alooma. Mai yayi mulki tsakanin 1571 da 1603 sannan yayi kanem-Barno tayi kaimi ta fadada har zuwa Katsina, Zamfara, Kano da wasu bangarori wanda yanzu suna cikin kasar Nijar wanda suka hada da; kanem Bakashe, Tasawa da Damagram.[1] Bakashe Bincike ya nuna shine sunan shugaban na al'ummar farko na yankin, Kanem kuma kalmar kanuri ce wadda take nufin Birni, Kanem Bakashe yana nufin Birnin Bakashe a yaren Kanuri kenan. Yankin yanzu ya kasance a cikin masarautun Maradi dake Jamhuriyyar Nijar. Sarkin Kanem Bakashe, Alhaji Sani, da babmahaifinshi Marigayi Sarki Daouda, sun kasance yan uwa ne na jin i ga Mai girma Wazirin Katsina na farko Sheikh Haruna kuma sun kasance suna zumunci na kwarai tsakanin ahalin waziri Haruna dake Najeriya. Haka kuma suma Ahalin Waziri haruna suna zumunci da su cikin Girmamawa da kaunar juna. Misali Marigayi Sarkin Kanem Bakashe Sarki Daouda ya hallarci Bikin Nadin Sarautar Wazirin Katsina, Prof.Sani Abubakar Lugga, kuma Sarki Sani na yanzu da ga Sarki Daouda yana kawo Ziyarar sada zumunci a kai a kai, Haka zalika Waziri Sani Lugga ya kasance ya hallarci Daurin Auren diyar Sarki Daouda a Kanem Bakashe kuma iyalan Waziri suma suna hallarta duk wani taro a Kanem Bakashe. Sheikh Haruna ya kasance Malamin Addinin Musulunci ne kuma kakkanin sa sun taimakawa Sheikh Usman Dan Fodiyo wajen yin Jihadi a 1804, Waziri ya yanke shawarar da ziyarci Katsina domin neman Ilimi da bincike, kamar yadda ya saba ziyartar sauran sassan Duniya domin neman Ilimi da yada shi kamar Mali, Senegal, da garuruwa na kusa kamar Dosso, Damagaram, da Kance. Katsina a wannnan lokacin ta kasance mafi shaharar Cibiyar Addinin Musulunci a kasar Hausa kuma bugu da kari tana dauke da Malamai kwarai da gaske. Sheikh Haruna ya iso Katsina a shekara ta 1897 kuma ya shaku da Durbin katsina Muhammadu Dikko da Sarki Abubakar, A wannan lokacin anyi gaggawar shaida shi a matsayin Babban Malami kuma shaharare A bangaren Addinin Musulunci a wannan lokacin wanda bai bukatar wani horo na musamman, hakan ya sa aka sakashi cikin jerin Sarakunan Katsina.Akwai manyan Masallatai guda Ukku a katsina a lokacin. Daya shine Babban Masalaci wanda yake a hedikwatar Jama'atul Nasrul Islam kusa da Fadar Sarkin Katsina wanda babban limamin Masarauta yake jagoranta. Na biyu yana kofar kaura wanda Mallam Barmo yake jagoranta, shi kuwa na Ukku yana Kofar Samri inda aka nada Sheikh Haruna a matsayin Liman Haruna. Liman Haruna da Durbi Muhammadu Dikko sun kasance sun shaku sosae da Sarkin Katsina Abubakar wanda lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka zo domin jan ragamar Shugabanci na yankin a 1903 karkashin Jagorancin Lord Lugard. Sarki Abubakar ya nada Durbi Dikko a matsayin mai kula da dukannin al'amurra shi kuma Liman Haruna a matsayin Babban Liman. ya kamata a sani cewa idan aka cire tura wa guda biyu dukkan sauran sojojin turawan sun kasance Musulmai ne yan Najeriya wanda aka dauke aiki karkashin Shedikwatar Sojoji dake karkashin turawa a Lojoja da Zungeru a yanzu jahohin Kogi da Niger. A lokacin Muhammadu Dikko ya zama Sarkin Katsina a 1906, Mutun na farko daya fara nadawa Sarauta shine Aminintaccen Abokinsa Sheikh Haruna a matsayin Wazirin Katsina na Farko, Wannan shi ya haifar da farko Daular Sarki Dikko da Waziri Haruna a katsina. Waziri Haruna ya kasance makusanci kuma mataimaki wajen kawo ci-gaba a mulki Sarki Dikko, haka zalika Sarkin Dawa Abubakar (Dan Waziri Haruna, Mahaifin Waziri Abubakar) shima ya aksance makusanci kuma mataimaki ga Sarki Usman Nagogo (Dan Sarki Dikko), Sarki Muhammadu Kabir (Jikan Sarki Dikko) shima ya kulla alaka mai karfi ta mutuntaka da aminci tsakaninsa da Waziri Sani Lugga (Jikan Waziri Haruna). Mahaifiyar Prof. Sani Lugga itace Hajiya Aisha, diyar Mallam Zubair, wanda da ne ga Kwamandan Baraden Jihadi, Uban dawakin Katsina Muhammadu Sani, wanda yayi aiki karkashin Sarkin Katsina Abubakar.
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan karatun Adinin Musulunci na Wajibi a kananan Shekaru, Wazirin katsina Prof. Sani Abubakar Lugga an saka shi makarantar Firamare inda ya cigaba da karatun addinin Musulunci tare da Ilimin boko. Ya samu nasarar samun shaidar jarabawa ta (West African School Certificate), da sakamako mai daraja ta daya a dukkan darussa daga Makarantar (Provincial Secondary School, Katsina a yanzu Government College Katsina) a 1968. Inda yake da zabi domin zuwa Babbar Makaranta inda zai samu kwallin zuwa Jami'a don yin digiri ko Dipiloma, Ya zabi kuma an dauke shi a Kwalejin Harkar Noma a Jami'a daya tilo kuma mai daraja a yankin arewacin Najeriya a wancan lokaci Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya, inda ya kammala karatun dipiloma a bangaren Harkokin Noma a 1970. Saboda sha'awarsa da Ilimi, Prof lugga ya sake shiga Makarantar Polythecnic MAi daraja kuma ita kadai a yankin arewa a wancan lokacin watau Kaduna Polythecnic, in da ya samu shaidar National Diploma a bangaren Kasuwanci da sakamako mai daraja a dukkan Darussa a 1975. Ya cigaba da karatunsa inda ya kara samun Diiloma daga Kabelmetal Electro Training, Hanover dake kasar Jamus, a 1985. Kaunar Ilimi ga Prof. Lugga wannan ya bashi dama samun shiga Jami'ar Illorin domin yin karatun Digiri na Biyu wato Masaters a Bangaren Gudanarwar Kasuwanci (Business Administration Executive Program) a ka kar karatu ta 1998/1999. Sannan ya samu dama ta musamman dayin rijista ta hanyar yin karatu mai dogon zango domin yayi karatu na digiri na biyu dana Ukku a hade a lokaci daya wato (Masters Degree da Doctorate Degree) a Jami'ar St. Clements, a British West Indies. Ya zabi yayi karatukan a hade tare da Jami'ar St. Clement dake Ingila wadda ta kasance tana da rijista da yarjewar da hadin gwiwar Kungiyoyin Turai domin Karatun mai Nisan Zango (British Association of Open Learning) a Landan. da kuma Kungiyar Jami'oi da Kwaleji ta Duniya, dake Washinton DC a Amuruka. Bayan kammala karatun cikin Nasara, Bincike da Byar da takardun nazari, ya samu shaidar kararun Digiri na Biyu a bangaren Gudanarwar Kasuwanci (Master of Business Administration Degree) a 2002 da kuma shaidar Digiri na Ukku a bangare Gudanarwa wato (Doctorate Degree in MAnagement) a 2003 daga Jami'ar St. Clement. Bayan kamar Shekaru Sha biyu (12) a shekara ta 2015, ya samu shaidar Digirin digir gir a bangaren FAlsafar Kwantar da Tarzoma wato ( Doctor of philosophy Degree in Conflict Management) daga Jami'ar Suan Juan, dake Costa Rica a kasar Amuruka. Ya hallaci tarukam karawa juna sani