Datuk Sapawi bin Ahmad (an haife shi a ranar 5 ga watan Yulin shekara ta 1956) ɗan siyasan Malaysia ne. Ya kasance tsohon memba na majalisar dokokin Malaysia na mazabar Sipitang a Sabah, yana wakiltar kungiyar United Malays National Organisation (UMNO) a cikin hadin gwiwar Barisan Nasional daga shekara ta 2008 zuwa watan Mayu 2018.
An zabi Sapawi a matsayin dan majalisa a zaben 2008, inda ya maye gurbin Yusof Yaacob na UMNO a kujerar Sipitang.[1][2] Kafin shiga siyasar tarayya, Sapawi ya kasance mataimakin minista a gwamnatin jihar Sabah.[1]