Jump to content

Sarauniyar Saliyo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Elizabeth II ta kasance Sarauniya ta kasar Saliyo daga shekarar 1961 zuwa 1971, lokacin da kasar Saliyo ta kasance mai zaman kanta. Ta kuma kasance mai mulkin wasu yankuna na yankunan kasashen Commonwealth, gami da United Kingdom . Matsayinta na tsarin mulki a Saliyo galibi an ba da shi ga gwamnan-janar na kasar Saliyo.

Kasar Saliyo ta zama kasa mai zaman kanta ta hanyar Dokar yancin Kai watau Independence a turance.ta Saliyo ta 1961, wanda ya canza mulkin mallaka na Burtaniya na Saliyo zuwa memba mai zaman kansa na Commonwealth of Nations . [1] Sarauniya Elizabeth II ta zama shugaban kasa da Sarauniya ta kasar Saliyo, kuma gwamnan janar wanda ke zaune a gidan jihar ne yake wakilta madadin ta a kowace jiha.

Duke na Kent ya wakilci Sarauniya a wasu bukukuwan 'yancin kai. Gimbiya Alexandra ta Kent ta wakilci Sarauniya a wani Taron godiya da aka gudanar a London a ranar samun yancin Kai wato Independence a turance ta Saliyo . A Freetown, Duke na Kent ya buɗe sabon Ginin Majalisar a ranar 26 ga watan Afrilu. Saliyo ta sami 'yanci a tsakar dare na 26-27 a watan Afrilu kuma daga baya a wannan rana Duke ya shiga cikin bude majalisar dokoki ta kasar, inda Duke ya ba da kayan aikin tsarin mulki ga Mai girma Sir Milton Margai, wanda ya sanya Saliyo tazama ƙasa mai zaman kanta. Daga baya Sir Maurice Dorman, Gwamna, ya rantsar da shi a matsayin Gwamna-Janar, wakilin Sarauniya, ta Babban Alkalin Beoku Betts .

  1. https://en.wikipedia.org/wiki/Queen_of_Sierra_Leone#cite_note-1