Sarki Abdurrahman Daura
Wazirin Daura Abdurrahman ne ya gaji mahaifinsa sarkin Daura Malam Musa a cikin Shekara ta 1911. Sarkin Daura Alhaji Abdurrahman ya yi shekara 55 a bisa gadon sarautar Daura. A wannan lokacin an sa mi muhimman canje-canje.
Ci-gaban Zamani
[gyara sashe | gyara masomin]A lokacin sarautar Sarki Abdurahman an sami ci gaba sosae da canje- canje na zamani, a lokacin ne aka bude makarantar elimantareta farko a kasar Daura. An bude wannan makaranta ne a cikin Daura. A cikin shekara ta 1934 aka cire Daura daga lardin kano, aka mayar da ita sabon lardin Katsina.[1]
Shekara 40 bisa Gadon Sarauta
Sarkin Daura Abdurrahman yayi bikin shekara Arba'in bisa gadon sarautar Daura a cikin shekara ta 1951. A cikin shekaravta 1959 Jihar Arewa ta sami mulkin kai. A shekara ta gaba wato 1960, Najeriya ta sami 'yancin kai daga mulkin mallaka na Ingila. A zamanin Sarki Abdurrahman, garin Daura ya sami ruwan famgo da wayar iska, aka kuma kara fadada ilimin zamani da buden dakunan shan magani. [2] Shekara 50 bisa Gadon Sarauta
A shekara ta 1962, Sarki Abdurahman ya cika shekara 50 a bisa gadon sarauta. An yi kasaitaccen buki a wannan lokacin.[3]
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Allah yayi wa mai martaba sarkin Daura Alhaji Abdurahman Dan Mjusa rasuwa a cikin shekara ta 1966. Allah ya jikan mai martaba Sarki.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://en.wikipedia.org/wiki/Daura_Emirate
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-11. Retrieved 2023-03-11.
- ↑ https://en.wikipedia.org/wiki/Daura_Emirate
- ↑ https://www.facebook.com/570672416363041/photos/sarkin-daura-abdurrahman-a-1952-lokacin-yana-dan-majalisar-sarakuna-a-kaduna/1169982316432045/