Jump to content

Shkrodan Mustafi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mustafi

Shkodran Mustafi (An haifeshi a ranar 17 ga watan Aprilu shekara ta alif 1992), tsohon dan wasan baya ne na kasar Jamus.

Mustafi ya fara buga kwallon kafa tun yana dan karami. Ya fara buga wasanni a samartakar sa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa Harmburger SV da kungiyar kwallon kafa ta Everton inda ya buga wasa daya a wasan da ya shigo daga baya kafin ya koma ƙungiyar ƙwallon kafa ta Sampdoria a shekarar alif 2012. Ya sanya hannu hsr na tsawon shekaru 5 a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ts Valencia a watan Ogusta 2014. Sai kuma ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal akan jumillar kudi £35 miliyan bayan shekaru 2. inda ya buga wasanni 151 a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal. Daga baya kuma ya koma gasar Bundesliga inda yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Schalke04, sai kuma gasar Laliga inda ya doka wasa a kungiyar kwallon kafa ta Levente.

A fannin kasa kuma Mustafi ya fara buga cikakken wasan shi inda suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta kasar Poland yayin da ya wakilci kasar tashi wato kasar Jamus a shekara ta alif 2014. Kuma yana daya daga cikin jerin yan wasan da suka buga gasar cin kofin duniya na shekarar alif 2014 da aka buga kuma sune suka samu nasara a gasar. Da gasar kofin FIFA Confederation wanda aka buga a shekarar alif 2017. Da kuma gasar UEFA Euro wanda aka buga a shekarar alif 2016.

Rayuwar Gida[gyara sashe | gyara masomin]

Mustafi dan asalin kasar Albaniya ne daga Gostivar kudancin Marcedonia ya tasa kuma yayi wayo a kasar Jamus. Saidai dan wasan ya rike shaidar zama dan kasa na kasashen biyu da Albaniya da kuma ƙasar Jamus.

Mustafi ya kasance yana yin addinin musulunci.[66]

A watan Yuli shekarar alif 2016 ya auri mata yar Tsatsan kasar Albaniya mai suna Vjosa Kaba a Gostivar.[63] Ma'auratan sun hafi diya mace inda suka sanya mata suna Noemi (an haifeta a watan Yuli 2007) sai kuma suka haifi namiji sau suka sa suna Amar wanda aka haifeshi a watan Junairu shekarar alif 2019.[67][68]

Girmamawa[gyara sashe | gyara masomin]

Arsenal

FA Cup: 2016–17, 2019–20[67][68]

EFL Cup runner-up: 2017–18[69]

UEFA Europa League runner-up: 2018–19[70]

Germany U17

UEFA European Under-17 Championship: 2009[71]

Germany

FIFA World Cup: 2014[72]

FIFA Confederations Cup: 2017[73]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

https://en.wikipedia.org/wiki/Shkodran_Mustafi