Shuga (kashi na 6)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Shuga (kashi na 6)
television series season (en) Fassara
Bayanai
Part of the series (en) Fassara Shuga (TV series)

Shirin Shuga Naija shiri ne na MTV da ke haskaka rayuwar matasa daga sassa daban-daban da kuma ilimintarwa kan jima'i da cututtukan da ake tattare da su, Kariyar Lafiya da sauransu.[1] Karo na shida na MTV Shuga Naija an shirya shi ne a cikin babban birnin Legas inda jama'a daga sassa daban-daban na zaune a matsayin mazauna wasu kuma don kasuwanci da ayyukan yi.[2] Wannan sabon shiri mai ban sha'awa yana yazo tare da rikice-rikice da yawa, dangantakar abokantaka da ke gab da wargajewa, iyalai suna gab da rabuwa saboda sirri. Kazalika ya fi mayar da hankali ne kan ilimantar da matasa musamman kan Ilimin Jima'i, Tsarin Iyali, Kariyar Haihuwa, rigakafin cutar kanjamau da sauransu.[3] Sanannu kuma masu kyaututtuka a fannin shirye-shirye suka dauka nauyin shirin wato Chris Ihidero, da Emma Uduma na SMAT Media.[4]

Takaitaccen Bayani[gyara sashe | gyara masomin]

MTV Shuga kashi na 6 wanda aka fara a ranar 22 ga watan Fabrairun 2018 a FilmHouse IMAX Cinema, Lekki, yana nuna ƙwararrun taurari da labari mai ƙarfi.[5] Starring Timini Egubson, Jemima Osunde, Rahama Sadau, Adebukola Oladipupo, Abayomi Alvin, da sabbin fuskoki da yawa kuma tare da wasan kwaikwayo daga YCee.[2]

Ana ɗaukar Shuga Naija a matsayin jerin fina-finan matasan da aka fi kallo a shiyyar Afirka tun lokacin da aka fara shi a 2019.[6] Sabbin fuskoki a wannan kashin wasa ta 6 sune Ozzy Agu, Rahama Sadau, Amal Umar, Yakubu Muhammad, Bolanle Olukanni, Funlola Aofiyebi-Raimi, Nobert Young, Bukola Oladipupo, Alvin Abayomi, da Helena Nelson tare da wasu sabbin fuskoki.[7] Masu bada umurnin shirin MTV series season 6 sun hada da daraktoci da suka samu lambar yabo, Tolulope Ajayi, Ishaya Bako da Tope Oshin an bayyana su a matsayin daraktoci.

MTV SHUGA kashi na 6 yana dauke da wani salo da ke nuna fitattun tituna, wuraren rawa masu kayatarwa tare da cunkoson babban birnin Legas tare da jihohin Arewa masu haskawa na Kano da Kaduna.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "MTV Shuga Naija Season 6 screens in Lagos". 2018-05-17. Retrieved 2021-11-03.
  2. 2.0 2.1 TV Series 6". Retrieved 2021-11-03.
  3. "MTV Shuga Naija Season 6 screens in Lagos". 2018-05-17. Retrieved 2021-11-03.
  4. "BHM (2018-02-23). "MTV Shuga Season 6 Launches In Africa With Lagos Premiere!". Medium. Retrieved 2021-11-03.
  5. TV Series 6". Retrieved 2021-11-03.
  6. BHM (2018-02-23). "MTV Shuga Season 6 Launches In Africa With Lagos Premiere!". Medium. Retrieved 2021-11-03.
  7. "Here is the cast of 'MTV Shuga' Naija (Season 6) coming in 2018 | YOMZANSI". www.yomzansi.com. 2017-09-20. Retrieved 2021-11-03.