Jump to content

Simon Bikindi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Simon Bikindi (an haife shi a 28 Satumba shekara ta 1954 ya mutu a 15 Disamba shekara ta 2018), ya kasance mawaki ne kuma marubuci ɗan Ruwanda, wanda a da ya shahara sosai a Ruwanda. Wakokinsa na kishin kasa su ne jerin wakoki a gidan rediyon kasar Rwanda a lokacin yakin watan Oktoban 1990 zuwa Yuli 1994 kafin Jam'iyyar Patriotic Front ta Ruwanda ta karbi mulki. Don ayyukan da aka yi a lokacin kisan kare dangi na Afrilu 1994 akan Tutsi, an yi masa shari'a kuma aka yanke masa hukunci saboda tunzura kisan kiyashi ta Kotun Hukunta Laifukan Ruwanda (ICTR) a 2008. Ya mutu sakamakon ciwon sukari a wani asibitin Benin a karshen 2018.

[1] [2] [3]

  1. Killer Songs. DONALD G. MCNEIL JR. The New York Times. 3 December 2008
  2. Indictment against Bikindi Archived 2022-10-13 at the Wayback Machine, from the ICTR, last amended 15 June 2005
  3. Rwandan singer on genocide charge. The Independent, 11 September 2006