Jump to content

Suleman Asonya Adokwe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Suleiman Asonya Adokwe ya kasance dan siyasar kasar Najeriya ne kuma dan majalisar dattawa mai wakiltar Nasarawa ta Kudu a majalisar dattawa. An haife shi a ranar 15 ga Fabrairu, 1954 kuma dan kabilar Alago ne.

Farkon Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan kammala karatunsa na sakandare, Adokwe ya tafi karatu na gaba, inda ya sami digiri na farko a fannin ilimin zamantakewa, Masters a fannin Nazarin aiki.Ya karanci fannin shari'a kuma ya sami digirin digirgir na shari'a daga nan aka kira shi zuwa Kungiyar Lauyoyin Najeriya.

Aiki da Siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Adokwe ya yi aiki a matsayin ma’aikacin gwamnatin jihar Nasarawa daga 1979 zuwa 1999. Ya kai matsayin Babban Sakatare, daga nan kuma aka nada shi Kean is human Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida daga 2003 zuwa 2006.[1]

Adokwe ya tsaya takarar sanata a gundumarsa ta Nasarawa ta Kudu a zaben 2007 kuma yayi Nasarawa lashe zaben a jam’iyyar PDP. Bayan ya hau kujerarsa a Majalisar Dattawa a watan Mayun 2007, an nada shi a kwamitocin Majalisar Dattawa, a fannin Tsaro da Leken Asiri, Sojojin Ruwa, Tsare-tsaren Kasa, Man Fetur da Kasuwan hannun Jari. Adokwe yana goyon bayan kungiyoyin kwadago, wanda ya ce zai iya bayar da kyakkyawar suka ga gwamnati, saboda shugabanninsu na gujewa cin hanci da rashawa da goyon bayan dimokuradiyya a cikin kungiyoyin. Adokwe ya sake tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Kudu a jam’iyyar PDP a zaben Afrilun 2011. An kuma zabar shi karo na biyu, inda ya samu kuri’u 108,844 yayin da Tanko Wambai na jam’iyyar CPC ya samu kuri’u 103,320. Adokwe ya sake tsayawa takara karo na uku a zaben Sanatan Nasarawa ta Kudu a shekarar 2015 a karkashin jam’iyyar PDP inda ya sha kaye a zaben a hannun Arc Salihu H. Egyebola na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 95,781 yayin da Adokwe ya samu kuri’u 91,760.

Bayan kammala zaben, Adokwe ya garzaya kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a jihar Lafia Nasarawa domin kalubalantar nasarar Arc Egyebola.[2] A ranar 12 ga Oktoba 2015 kotun ta yi watsi da karar Adokwe saboda rashin cancanta. Da rashin gamsuwa da hukuncin, Adokwe ya garzaya kotun daukaka kara a jihar ta Markurdi Benue, daga bisani kotun daukaka kara ta tabbatar dashi matsayin wanda yayi nasara. Daga nan ne kotun ta umarci INEC da ta mayar da Sanata Adokwe a matsayin zababben dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu.