Superstar (2015 fim)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Superstar (2015 fim)
Asali
Lokacin bugawa 2015
Ƙasar asali Najeriya
Characteristics

Superstar fim ne na Nollywood wanda wani ɗan asalin ƙasar Amurka haifaffen Najeriya ne furodusa Toni Abulu shugaban kamfanin Black Ivory Limited, wani kamfanin nishaɗi da ya shafe shekaru 30 a harkar fim ya shirya kuma ya ba da umarni. Fim ɗin yana nuna labarin wani mawakin Najeriya (Tekno) wanda ya yi gwagwarmaya a masana'antar kiɗan Najeriya. An ƙaddamar da fim ɗin a ranar 5 ga Yuni, 2015 ta hanyar rarrabawar Silverbird. Fim din ya hada da matasa mawakan Najeriya Tekno da Iyanya wanda ya zama wasn kwaikwayonsu na farko da ya fito a shirye shiryen talabijin. [1]

Tsokaci[gyara sashe | gyara masomin]

Tekno ya fito (a matsayin Modele ko Dele) da abokinsa ( manajansa, Ovie) a cikin fim ɗin sun daina karatu daga jami'a don yin sana'ar kiɗa. Dole ne ya fuskanci matsaloli masu yawa da suka fara daga danginsa waɗanda ba su yarda da ra'ayin sana'ar kiɗa ba. Tekno ya ci karo da wata dama ta gabatar da wani faifan bidiyo ga wani furodusa dan Amurka da ke neman hazikan matasa a Najeriya. An fito da Toyin Aimakhu a cikin fim din a matsayin mahaifiyar Tekno kuma shine karo na farko da ta fara yin rawar turanci jn a fim.

'Yan wasan shirin[gyara sashe | gyara masomin]

Manyan jaruman fim din su ne;

  • Tekno (a matsayin Modele ko Dele)
  • Ovie a matsayin Ushebebe
  • Toyin Aimakhu
  • Steph Nora Okere

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0