Jump to content

Sylvanus Olympio

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 


Bayan Ya kammala karatunsa daga Makarantar Tattalin Arziki ta London, ya yi aiki a Unilever kuma ya zama babban manaja na ayyukan Afirka na wannan kamfanin ba Unilever. Bayan Yaƙin Duniya na biyu II, Olympio ya zama sananne a kokarin samun 'yancin kai na Togo kuma jam'iyyarsa ta lashe zaben Shekarar 1958, ta inda ya zama Firayim Minista na kasar. Ikonsa ya kara karuwa lokacin da Togo ta sami 'yancin kai kuma ya lashe Zaben shekarar 1961, wanda ya sanya shi shugaban farko na Togo. An kashe shi Olympio a lokacin juyin mulkin Togo na 1963.