Taimama
1. Ma’anarta, a harshen Larabci da kuma Shari’ah. [1]
a. Ma’anarta, a harshen Larabci, shi ne: Nufi da dogara.
b. Ma’anarta, a Shari’ah; shafar fuska da hannuwa da turbaya mai tsarki akan a siffa kebantacciya. Kuma yana daga cikin abun da Allah ya kebanci wannan al’umma da shi, wato madadin amfani da ruwa.
2. Wanda aka yardar wa ya yi Taimama?.
[gyara sashe | gyara masomin]1. Rashin ruwa ko nisansa.[2]
2. Idan mutum yana da ciwo ko rashin lafiya, kuma yana tsoron cutarwa idan ya yi amfani da ruwa.
3. Idan ruwa ya kasance mai sanyi sosai kuma bai samu abun da zafafa shi ba, (wato zai dunduma).
4. Idan ya bukaci ruwan sha ko waninsa, kuma yana tsoron kishi zai iya yi masa illa ga kuma ruwan kadan ne, to sai ya yi taimama.
3. Sharuddan wajabcin taimama
[gyara sashe | gyara masomin]a. Balaga.[3]
b. Ikon samun amfani da turbaya.
c. Samuwar hadasi wanda ya warwara alwalar.
4. Sharuddan ingancin taimama
[gyara sashe | gyara masomin]1. Musulunci[4]
2. Yankewar jinin al’ada ko biki.
3. Hankali.
4. Samun wuri mai tsarki.
5. Farillan taimama
[gyara sashe | gyara masomin]1. Niyya.
2. Wuri mai tsalki.
3. Bugu na farko.
4. Shafar fuska da tafikann ha nnuwa.
6. Sunnonin taimama
[gyara sashe | gyara masomin]1. Bismillah. ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ
2. Fuskantar alkibila.
3. Ta kasance ayi ta a lokacinda za’ayi sallah.
4. Bugun kasa na biyu.
5. Jerantawa.
6. Tsattsefe yatsun hannu.
7. Abubuwan dake warware taimama
[gyara sashe | gyara masomin]1. Samun ruwa.
2. Abubuwan dake warware alwala da wanka to suna warware taimama, domin ita taimama abar musanyawarsu ce, kuma abunda ya warware na asali (wato alwala da wanka) to yana warware na biye da shi.
8. Yadda ake taimama
[gyara sashe | gyara masomin]Sai mutum ya yi niyya, ya ambaci sunan Allah (ya ce: ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ), sai ya bugi kasa da hannuwansa, sa’annan fuskar shi da tafikan hannuwansa da turbayan a jere.
9. Taimama ga mai dauri ko ciwo
[gyara sashe | gyara masomin]Duk wanda akwai karaya ko ciwo ko kurji a jikinsa, kuma yana tsoron cutuwa idan ya wanke wajan da ruwa, ko kuma zai sa shi damuwa idan ya shafa, to sai ya yi taimama bayan haka sai ya wanke sauran. Duk wanda ya rasa ruwa ko turbaya a kowanni hali to sai ya yi sallah gwargwadon halin kuma ba zai sake ta ba.