Takalmi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
takalman yara.
takalmin zuwa aiki.
takalmin fita gudu.
Takalmin Mata na daki.
takalmin fada.
takalmin sandal.

Takalm: shi ne abunda mutane suke sakawa a kafafuwan su (sawayensu), domin kariya daga hakurra irin na daya da kwalba da kuma daukar cututtuka.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Kalmar takalmi, ta samo asali ne daga fadi wasu cewa asalin kalmar ita ce " taka lumi" ma'ana ka taka kasa cikin kwanciyar hankali, ba tare da tunanin wani abu zai same ka ba, ko za ka taka wani abu ba.

Rabe-raben takalma[gyara sashe | gyara masomin]

takalmin kwallon kafa.

Takalma nau'insu na da yawa akwai takalmin shiga ruwa da yaki dana bayi da gini da shiga daji da bacci da na gudu da na kwallo da na motsa jiki da kuma mai dogon diddige ( hill). Kuma akwai wadanda suka kebanta da mata da kuma na maza da na yara da na manya da dai sauransu. Akwai takalmi kala sittin da hudu kamar yadda bincike ya tabbatar.[1].[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://threadcurve.com/types-of-footwear/
  2. https://www.shoezone.com/Womens/Womens-Shoe-Styles