Jump to content

Tarihihi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Tarihihi nau'i ne na labari na gargajiya wanda ya kunshi labarai wadanda suka shafi wadansu ayyukan mutane wadanda ake tsammanin ko ma ake da tabbacin cewa sun faru a tarihi. Irin wadannan labaran suna koyar da tarbiyya, suna kuma da wata kima da za ta sa a yarda da cewa gaskiya ne. Wasu daga cikin abubuwan da suka faru a tarihihi sun kunshi abubuwan ban al'ajabi. Cigaba da bayar da labaran tarihihi na kara gyara su da tabbatar da su.

Yawancin labaran tarihihi ana masu kallon rashin tabbas na afkuwarsu, wato ba kowane abu ne nasu mutane suka yarda da shi ba, amma kuma ba komai a cikin labarin ke ba a yarda da shi ba. A wadansu lokuttan ana rarrabe tarihihi da tatsunniya ta hanyar gane cewa a tarihihi taurarin labarin mutane ne ba gumaka ko alloli ba. Sannan kuma suna dauke da wani burbushin wani abu da ya faru a tarihi a lokacin da a tatsunniya ba a samun hakan. Brothers Grimm sun fassara tarihihi da cewa "labari ne na gargajiya da yake da wani dandano na tarihi." Wato wani ragowa ne na "damuwa da halin da mutane suke ciki" ta yadda aka samu wadanda aka bayar da tarihihinsu da yawa, abinda bai bar "wata shahararriyar shakka ba", wanda hakan ke tabbatar da cewa tarihihi "yana da dandanon tarihi".

Tarihihi, a taƙaice kuma kai tsaye, shi ne tarihin da ya jirkice. Masana harshen Hausa da suka haɗa da, Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, Dakta Mu’azu Sani Zariya, da kuma Dakta Tanimu Musa ‘Yar’aduwa, sun bayyana wannan kalma da cewa:

Kalma ce da aka tsago ta daga kalmar “tarihi”, ta hanyar yi mata ƙarin ɗafe da gaɓar ‘”hi”, sai ta zama “Tarihihi”. Sannan kuma suka bata ma’ana ta, “Gurɓataccen tarihin da aka cakuɗa shi tsakanin gaskiya da ƙarya, aka cusa masa labarai marasa kan gado, na soki burutsu, har ya fita daga ainihin tarihin lamarinsa na gaskiya, ya wofinta daga siffarsa ta asali”.

Dalilin jikirtar irin wannan tarihi ya koma tarihihi shi ne hanyar isar da shi, wacce aka fi sani da kunne ya girmi kaka. Wato, tarihi ne da ake isar da shi da ka, wanda kuma ya jirkice tun kafin a fara rubuta shi. daga cikin misalan irin waɗannan tarihihi akwai tarihin Bayajidda na ƙasar Hausa, tarihin sarauniya Amina, da sauran makamantansu, waɗanda abu ne mai matuƙar wahala a tantance gaskiyar lamarin, koma ana iya cewa tantancewar ba za ta yiwu ba.

Amma fa duk da haka an yarda da cewa wannan tarihihi, yana taimakawa manazarta wajen samun bakin zaren tarihi a inda ya ƙulle.

Manazarta:[gyara sashe | gyara masomin]


Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.