Tarihin Sharahbil Muhammad Sani
Tarihin Sharahbil Muhammad Sani |
---|
An haifi Sharahbil Muhammad Sani a garin Makera da ke karamar hukumar Mulki ta Birnin Kebbi, ya yi karatunsa a garin Birnin Kebbi ya kuma ci gaba da harkar rubuce-rubuce domin fadakar wa da tunatar da al'umma.Sharahbil mutun ne mai hakuri da juriya da tausayawa al'ummarsa. Ya yi rubuce-rubuce kala daban-daban daga ciki akwai littafan da ya rubuta kamar: ...Mabudin Wahala, Kashedinku Mashaya!!!, Addu'a daga Alkur'ani da Hadisi Hausa da kuma Turanci, Addu'a don masu karatu da Jarabawa (Hausa da turanci) Mizani na Asali kan kimiyyar kwamfuta don makarantun sakandare da jami'o'i a cikin harshen Hausa. A bangaren littafan soyayya kuma, Sharahbil Muhammad Sani ya bada gudummawarsa ga masoya, inda ya rubuta littafi mai suna Lafazin Soyayyah da Maganganun Hikima kan so. ya kuma rubuta littafai don nishadi kamar ... Talaka dariyar Mai Ragg, Littafin karin magana mai suna KARIN MAGANA 200 da hausawa ke amfani da su. Sharahbil ya bada gudummawa sosai wajen taimakawa matasa a ya kuma kirkiro wata ƙungiyar marubuta mai suna Pen Writers Association, ya kirkiri kungiyoyi da dama don taimakawa al'umma. Muna fatar Allah Ya taimake mu ya kuma kare mana shi Ya albarkaci rayuwar shi da kuma ta iyalinsa da yan uwansa da masoyansa gabaki daya amin.