Jump to content

Tarihin kasar hadejia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Asalin sunan Hadejia Ya farune daga wani maharbi mai suna Hade, shi wannan maharbi ya taho ne daga yankin Machina ya yiwo yamma har yazo wannan wuri da yanzu ya zama Hadejia. Lokacin da yazo sai ya iske Daji mai bishiyoyi ga kuma Namun Daji da Tsuntsaye ta ko ina, sai ya zauna yaci gaba da farautarsa har saida wata rana yana tafe da karyar sa sai tayi nisan kiwo ko da tazo sai yaga duk jikinta da ruwa, sai yayi mamakin hakan har ma sai yabi sawunta. Koda yaje sai yaga kogi kuma ga tsuntsaye suna shawagi a wurin. Sai ya yanke shawarar zama a wannan wurin, kuma hakan yayi. Anan ya zauna yayi bukkarsa yake harbe harben Namun daji kuma yayi SU,wato kamun kifi.

In ya kashe namun daji sai yaje ya sayar da fatun. Harma ya dauko matarsa wato Jia ya dawo da ita wannan wurin. Kuma mutane sai suke zuwa sayen fatu da nama a wurinsa. Duk wanda yazo wurin sai yayi sha'awar zama a wurin, haka nan gari ya fara bunkasa wasu maharba, wasu masinta, wasu kuma mafarauta. Sai gari ya kafu kowa yazo wucewa sai ya yada zango a garin. Kuma makwafta masu zuwa sayen Namun Daji sai suke kiran garin da suna Garin Haden-jia, wato suna masa lakabi da sunan matarsa.

To kasancewar gari sai da shugabanci ne yasa shi Hade ya zama shugaban garin, duk wanda zaije sayen fatu ko nama sai yace na tafi garin Haden jia.

Wato ana masa lakabi da sunan matarsa. To sakamakon takaita kalma irin ta Bahaushe sai aka dunkule sunan ake cewa Hadejia.

Kuma bayan zamanin wannan mutumin

Hadejia taci gaba da zama gari kuma tare da shugabanci wato mulkin Sarakunan Habawa. Kuma a lokacin akwai kananan Garuruwa masu wadda suke kusa da Hadejia kamar Rubban Dakata, Auyo, Hadagwaigwai da dai sauransu. Wadanda suma suna da nasu sarakunan a wannan Lokacin. Kuma Hadejia sunyi Sarakunan Har guda talatin da biyu(32),amma sunan mutum uku ake dasu wadanda sukayi mulki kafin zuwan Fulani.

1, BAUDE

2,MUSA

3, ABUBAKAR.

A zamanin Mulkin Sarkin Hadejia na Habe Abubakar fulani sukazo kasar Hadejia, kuma shine ya basu masauki a Hadejia Lokacin Hadejia tana karkashin Daular Borno, domin tana karbar Umarni ne daga Galadiman Borno. Sarkin Hadejia na Habe shi ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin Hadejia. Wato kafin Jihadin Shehu usman Danfodiyo. Kuma har yanzu fulanin sune suke sarautar Kasar Hadejia.

wananan shin ka dan daga cikin tarihin kasar hadejia.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]