Jump to content

Tatsuniyoyi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.


Tatsuniyoyi


  • Gizo da Noman Gyaɗa
  • Gizo da Saniya
  • Gizo da Ƙoƙi da Kantu
  • Gizo da Ɗanrago...
  • Gizo Ɓarawon Gyaɗa
  • Gizo da Ɓaure
  • Biri da Kura
  • Kura da Kare
  • Auren Barewa...
  • Kuturu, Makaho...
  • Alhaji da Hajiya
  • Wasu Mutane Huɗu
  • Baban Rogaji
  • Yarinya da Ƙawayenta
  • Mutum da Zabi
  • Ƙuda da Kwaɗo
  • Ɓarayin Rake
  • Maraya
  • Ɓarawon Gwal
  • Tsiniyama da Lafiyana
  • Yusufu da Bala.

Tatsuniya: Gizo da Noman Gyaɗa

[gyara sashe | gyara masomin]

Wata rana Gizo da Ƙoƙi, abin duniya ya yi musu zafi. Sai Ƙoƙi ta ce da Gizo, “Ina ga da za mu yi noma da mun samu sauƙi”. Da Gizo ya ji haka sai ya ce, “Ƙwarai hakan ya dace”. Sai Ƙoƙi ta ce, “to me ka ke ganin zamu noma? Mu shuka shinkafa ne, ko alkama, ko kuma acca?” Sai Gizo ya ce, “a’a, mu shuka gayaɗa kawai”. Sai suka yarda akan cewa za su shuka gyaɗa. Amma ashe shi Gizo yana nufin ya yiwa Ƙoƙi wayo da wannan shawara tasa.

Da aka tashi yin shuka, sai Gizo ya ce da Ƙoƙi, ai ba a shuka gyaɗa sai an soya ta. Sai Ƙoƙi ta amince ta soya gyaɗa, ta baiwa Gizo ta ce ya je ya shuka. Da Gizo ya je gona dan yin shukar gyaɗa, sai ya ɗaura lilo a jikin bishiya, ya hau lilon nan yana cin gyaɗa, yana rera waƙa kamar haka:

……………………….

Da haka-da haka, yau ya je gona, gobe ya je, har wannan gyaɗa ta ƙare, ba tare da ya shuka ba.

Da damina ta yi nisa, sai ƙoƙi ta fara tambayarsa maganar gona, shi kuwa Gizo sai ya hau bada labari yana cewa, “Ai gonar nan ta yi kyau sosai”.

Da kakar gyaɗa ta fara yi, sai Ƙoƙi ta ce da Gizo ya fara ciro musu wannan gyaɗa su riƙa ɗan taɓawa kafin a farɗe ta. Saboda haka a duk lokacin da Ƙoƙi ta buƙaci gyaɗa sai Gizo ya je gonar mai gari ya yago ya kai mata. Sannu a hankali Gizo ya kusa cire gyaɗar gonar mai gari baki ɗayanta.

Wata rana sai mai gari ya gane cewa ana cirar masa gyaɗa, saboda haka sai ya zuba masu gadi a gonar suka ɓoye a gurin da ba mai ganinsu. Can sai ga Gizo ya zo cirar gyaɗa. Caraf, masu gadin nan suka cafke Gizo, suka tafi da shi gurin mai gari. Daga nan aka yanke masa hukunci, aka kore shi daga gari.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.

Tatsuniya: Gizo da Saniya

[gyara sashe | gyara masomin]

Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

A wani gari, an yi wata Saniya mai ciki. Wata rana wannan saniya tana cikin shan ruwa a rafi, sai ta haifi ‘ya’ya guda huɗu, uku daga cikinsu mata ne, ɗaya kuma namiji. Bayan da ta gama shan ruwanta, sai ta fito da ‘ya’ya matan nan guda uku, ɗayan kuma wanda shi ne namiji, sai ta bar shi a cikin ruwan.

Bayan ta fito da su daga ruwan nan sai ta samu guri ta ɓoye su, ita kuma ta tafi kiwo. Da ta je kiwo ta samu abinci ta ci, ta kuma kawo wa ‘ya’yan nata.  Da ta iso bakin rafin nan sai ta rera waƙa tana kiran ‘ya’yan nata, tana cewa:

Sari’atul-ma zo ki ci, mazariƙi-mazandamu ma zo ki ci, maza-dandama ma zo ki ci, amma kai na cikin ruwa ban da kai.

Shi ke nan da ‘ya’yan saniyar nan suka ji haka sai suka fito suka ci abincin nan suka sha ruwa, suka kwanta. Ita kuma saniyar nan sai ta sake barin ‘ya’yan nan nata ta tafi kiwo. Da ta je, sai ta ci ta ƙoshi, sannan ta ɗebo wa ‘ya’yanta. Da ta zo sai ta sake cewa:

Sari’atul-ma zo ki ci, mazariƙi-mazandamu ma zo ki ci, maza-dandama ma zo ki ci, amma kai na cikin ruwa ban da kai.

Da ‘ya’yan saniyar nan suka ji, sai suka fito, suka ci abinci suka sha ruwa, suka kwanta. Ashe Gizo yana laɓe yana ganin abin da ke faruwa. Ai kuwa saniyar nan na tafiya, sai Gizo ya fito, ya kama rera waƙa. ‘Ya’yan saniyar nan suna ji, amma suka ƙi fitowa saboda Gizo ba daidai yake waƙar ba. Da Gizo ya ga sun ƙi fitowa, sai ya tafi ya sake laɓewa. Can bayan wani lokaci sai ga saniya ta sake dawowa. Tana zuwa sai ta kama rera waƙa kamar yadda ta saba yi: Sari’atul-ma zo ki ci, mazariƙi-mazandamu ma zo ki ci, maza-dandama ma zo ki ci, amma kai na cikin ruwa ban da kai.

Da ‘ya’yan saniya suka ji ita ce, sai suka fito suka ci abinci sannan suka sha ruwa suka sake komawa suka ɓoye. Ita kuma saniya ta sake tafiya kiwo.

Bayan tafiyar Saniya ba da jimawa ba, sai Gizo ya sake fitowa. To, yanzu Gizo ya haddace abin da saniyar nan take faɗa, saboda haka yana rera waƙar nan, sai ‘ya’yan saniyar nan suka fito. Suna fitowa sai Gizo ya kama su ya gudu da su, ya cinye.

Can bayan wani lokaci sai saniya ta dawo daga kiwo da abincin ‘ya’yanta guda uku. Da ta zo, ta yi waƙa, ta yi waƙa, ta yi waƙa, amma shiru ba ta ga kowa ba. Can sai ta juya ta ce: To kai na cikin ruwa zo ka ci. Shi kuma sai ya ce, “Ni na cikin ruwa ba ni ci, alherin Allah ya ishen”. Da Saniya ta ji haka sai kawai ta faɗi ta mutu.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.