Jump to content

Tolulope Popoola

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Tolulope Popoola marubuciya ce 'yar Najeriya wacce ta ƙware a cikin rubutun Littattafan soyayya. An nuna rubuce-rubucenta da sassan labaranta a cikin wallafe-wallafe da mujallu da yawa.

Popoola ta fara rubutu a shekara ta 2008, bayan ta yi murabus daga aikin da take da kamfanin lissafi. Ta rubuta littafinta na farko a shekara ta 2009, amma ta yanke shawarar bazata wallafa ba bayan ta gano cewa ya yi kama da In Dependence na Sarah Ladipo Manyika . A shekara ta 2012, ta wallafa Littafin soyayya na farko, Nothing Comes Close . Littafin an jera shi a matsayin daya daga cikin littattafai mafi kyau na 2012 a kungiyar African Writers Club.

[1] [2]

  1. bivan, Nathaniel (March 5, 2016). "Why I quit accounting for writing, publishing – Tolulope Popoola". Dailytrust. Retrieved 2018-08-04.
  2. Babatunde, Olamide (May 13, 2017). "Tolulope Popoola: I used myself and novel as experiment". Daily Sun. Retrieved 2018-08-04.