Tsamiya
Tsamiya | |
---|---|
Conservation status | |
Least Concern (en) (IUCN 3.1) | |
Scientific classification | |
Kingdom | Plantae |
Order | Fabales (en) |
Dangi | Fabaceae (en) |
Tribe | Amherstieae (en) |
Genus | Tamarindus (en) |
jinsi | Tamarindus indica Linnaeus, 1753
|
General information | |
Tsatso | Tamarind seed oil (en) , tsamiya da tamarind (en) |
Tsamiya bishiya ce mai amfani sosai. Bincike ya tabbatar da cewa dukkanin jikin bishiyar tsamiya yana da amfani sosai ga lafiyar Dan Adam (Masset, Candia da Ocheng, 2015; Gilma da Watson, 1994; Muzaffar da Kumar, 2017), wanda ka iya zama amfanin abinci, magani, kayan aiki kamar katako ko makamashin wuta.[1]
Asali
[gyara sashe | gyara masomin]Bishiyar tsamiya 'yar asalin Yammacin Afirka ce (Muzzafar da Kumar, 2017;
Massete, Canadia da Ocheng, 2015).[2]
Sunayen Tsamiya a wasu yarukan
[gyara sashe | gyara masomin]Asalin sunan tsamiya a kimiyyance shi ne Tamarindus Indica L. A Turance kuma sunanta Tamarind. Larabawa kuma suna kiranta da Tamri hindi ( ﺗَﻤﺮِ ﻫِﻨﺪِﻯ ).[3]
Wuraren da aka fi samun tsamiya
[gyara sashe | gyara masomin]Tsamiya, bishiya ce wacce take iya rayuwa a cikin zafin hamada mai tsanani, matsakaici da ma guraren da basu da zafin. Guri guda da tsamiya ba ta iya rayuwa a gurin shi ne guri mai gishiri. Wannan dalilin ne ya sa bata iya rayuwa a bakin teku saboda haka ta zamo bishiyar daji amma bata cika rayuwa a cikin kurmi ba. Amma duk da haka akwai ƙasashen da ake yin gonarta a reneta don amfanin jama'a.[4]
Sassan Jikin Tsamiya
[gyara sashe | gyara masomin]- Saiwa: Ana amfani da saiwar tsamiya wajen haɗa magungunan gargajiya.
- Gangan Jiki: Shi ne abin da ya fito daga ƙasa har zuwa rassa, abin da za a iya kira itace ko iccen tsamiya. Ana amfani da shi wajen yin katako domin gini. Rassan kuma ana rufin ɗaki da su. An tabbatar da cewa gara bata cin katakon da aka yi daga itacen tsamiya. Sannan kuma ana yin makamashin wuta da itacen tsamiya, kai tsaye ko kuma ta hanyar yin gawayinsa, kuma gawayin itacen tsamiya yana jimawa yana ci (ba kamar sauran ba da suke ƙonewa dawwuri).
- Ganye: Ana amfani da ganyen tsamiya a matsayin abincin dabbobi. Sannan kuma ana haɗa magani da ganyen tsamiya a kimiyyance da kuma gargajiyance.
- 'Ya'yan Tsamiya: Shi ne sashe mafi muhimmanci a jikin tsamiya. Domin a same shi ake shuka ta. Dukkan amfaninkan tsamiya da kuma sinadaran da ake samu a jikin tsamiya da za a zayyano a ƙasa a kansu za a yi magana.
- Kwanson ‘Ya’yan Tsamiya: Ana amfani da shi wajen haɗa magani.
- Ƙullon Tsamiya: A cikin ‘ya’yan tsamiya idan aka cire kwanson, aka fito da asalin ‘ya’yan, suma a cikinsu akwai ƙullo; wato irin tsamiyar kenan. Da shi ake sake samar da wata tsamiyar. Sannan kuma a kimiyyance ana yin roba da su sannan kuma akwai wani sinadari da ake kira fektin (Pectin) wanda ake saka shi a cikin magani domin ya bai wa magani kariya daga lalacewa.
- Fure: Ana kiwon zuma da furen tsamiya saboda tana matuƙar son ƙamshin. Sannan kuma dai ana haɗa magani da shi.
- Tsoka: Tsokar ‘ya’yan tsamiya ana amfani da ita a gargajiyance wajen fitar da tsatsa daga jikin abubuwan da suka haɗa da zinare, azurfa, tagulla da sauransu.
Kiwon Lafiya
[gyara sashe | gyara masomin]Amfanin tsamiya a ɓangaren abin da ya
shafi kiwon lafiya ya haɗa da:
- Narkar da abinci.
- Saka jiki hutu.
- Ƙarin jini.
- Saukar da gudn jini, kasantuwar tana ɗauke da sinadarin fotashiyom. Wannan sinadari kuma zai taimaka wa masu hawan jini wajen rage wa jinin gudu har ya hana shi hawa. Sannan kuma wanda ba shi da wannan larura to zai samu kariya daga hawan jini.
- Taimaka wa jijiya ta yi aiki. Sinadarin siyamin (Thiamin) da yake a cikin tsamiya shi yake taimaka wa jijiya ta yi aikin da ya dace a cikin jikin ɗan’adam.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Muzaffar K. da Kumar P. (2017). Tamarind a Mini Review. Department of Food Engineering and Technology, Sant Longowal Institute of Engineering and Technology, Longowal, Punjab-148106, India. MOJ Food Processing & Technology.
- ↑ Masette M., Candia A. da Ocheng A. G. (2015). The Commercial Viability of Tamarind (Tamarindus indica L) Fruit Based Products for Improved Incomes Among Farmers in Northern and Eastern Uganda. Agricultural Engineering and Appropriate Technology Research Centre (AEATREC), P. O. Box 7065 Kampala, Uganda. African Journal of Food Science and Technology, ISSN: 2141-5455, Vol. 6(6) pp. 167-176, September, 2015.
- ↑ http://m.frmina.in[permanent dead link]
- ↑ Sahoor R. da Sahoor S. (2015). Natural Polymer of Tamarind Seed: A Prospective Carrier for Ocular Drug Delivery. Melaka Manipal Medical College, Malaysia. European Scientific Journal September 2015 edition vol.11, No.27 ISSN: 1857 – 7881.
- ↑ Edward F. Gilman and Dennis G. Watson (1994). Tamarindus Indica. Tamarind Fact Sheet ST-618, October, 1994.