Tsangaya
Appearance
Tsangaya wani tsari ne na gurin da ake bada karatu da tarbiyyar Musulunci kuma kalmar Tsangaya ta Hausa ce a zahiri tana nufin Cibiyar Koyo. Wanda yake zuwa makarantar ana kiransa da Almajiri.Haka zalika tsangaya tana nufin wata matattara ko gurin koyon karatu, kalmar Hausa ce wacce ta samo asali daga kalmar larabci “Almuhajirun”, ma’ana dan hijira. Yawanci ana nufin mutumin da ya yi hijira daga jin dakin gidansa zuwa wasu wurare ko wani mashahurin malami wajen neman ilimin addinin Musulunci.[1]