Tsibirin Seychelles
Appearance
Jamhuriyar Seychelles tsibirin Tekun kasar Indiya ne a Kudancin yankin nahiyar Afirka. Tana da yawan mazauna kasa da adadin kimanin 100,000 kamar watan Mayu, shekarar 2024. Tana da gaurayawan kabila na Afirka, Indiyawa, farare, Sinawa, gaurayawan jinsi, da kuma turawa. Yawancin attajirai turawan Afirka ta Kudu sun yi ƙaura zuwa wannan tsibiri. Har ila yau, sun gina wani karamin birnin tsibiri daga filin da aka kwato a cikin teku, tare da wata gada da ta hade shi da babban tsibirin Mahe. Seychelles tana da manyan tsibiran guda uku, waɗanda ake kira Mahe, Praslin, da La Digue. Babban birnin Seychelles shine Victoria wanda ke arewa maso gabashin gabar tekun Mahe Island.