Tuwon dawa
Appearance
Tuwon dawa
[gyara sashe | gyara masomin]Tuwon dawa wani nau'in Abincine na ƙasar Arewa.Shidai wannan tuwo ya samo asaline tun wajen iyayenmu da kakanni. Ana yin shi ne da garin dawa, wanda ke ba shi launin ruwan kasa da sinadarai. Ana iya cin Tuwon dawa da kowace miya, amma ya fi kyau da miyar okra koh miyar yauki kamar kuka da kubewa dama dai sauransu YADDA AKE YI Dawa Kanwa Da farko dai zaka samu dawarka akai a nika ,idan an nikoh sai a tankade sai a wanke tsakin asa ruwa a takunya ya tafasa sai a talga sai asa yar kanwa yar kadan ajira ya dahu sai asa garin a tuka sai abashi yan mintuna ya silala