Ulan Bato[1] ko Ulaanbaatar (Turanci) ko Oulan-Bator (Faransanci), da harshen Mangoliya Улаанбаатар, birni ne, da ke a ƙasar Mangoliya. Shi ne babban birnin ƙasar Mangoliya. Ulan Bato yana da yawan jama'a 1,444,669, bisa ga jimillar 2018. An gina birnin Ulan Bato a shekara ta 1639 bayan haihuwar Annabi Issa.