Jump to content

User:Abdoullameen

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hausa al'umma ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya,da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Al'umma ce mai dimbin yawa, sun bazu a cikin kasashen Afirka. Da kasashen larabawa, kuma a al'adance masu matukar hazakane, akalla akwai sama da mutane miliyan hamsin wadanda harshen Hausa shi ne asalin yarensu. A tarihi kabilar Hausawa na tattare a salsalar birane watau alqarya. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai, Borno, da kuma Fulani, a karni na 19 Hausawa suna amfani da Doki ne domin yin sifiri da balaguro.