Jump to content

User:Baban Narjis

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sunana Salisu Tukur Sadiq, amma ina amfani da Salisu Tukur Gaiwa, a rubuce-rubucena (pen name), ni mutum ne mai sha'awar karatu da rubutu tun ina karami. A yanzu kuma sha'awar tawa ta yi yado zuwa sha'awar fassare-fassare, musamman ma daga Harshen Turanci zuwa Harshen Hausa. Na fassara wadansu littattafai daga Turanci zuwa Hausa wasu daga cikinsu ma na ilmin kimiyya ne kamar LAFIYARKA BABBAN JARINKA da MATAKAN KARIYA DAGA SHAN MIYAGUN KWAYOYI. Na kuma rubuta wadansu littattafan da suka shafi sana'ar Kira da kuma na shagube (satire) a Harshen Hausa da na Turanci. Na kasance Editan Mujallu guda biyu: MUJALLAR MANOMA da kuma ATTAJIRAH. Ina da Digiri a Harshen Hausa (B A Hausa), a yanzu kuma ina karatun digiri na biyu (M A Hausa), duk a Jami'ar Umar Musa Yar’adua, Katsina.