Wikipedia talk:Hakkin Maraya

Page contents not supported in other languages.
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga User:Bello Yusha'u)

HAKKIN MARAYU A MUSULUNCI !! Babu na daya

Bismillahir-Rahmanir-Raheem, wa salallahu alan-Nabiyyil-karemm, Bayan haka, hakika marayu suna da hakkoki a musulunci masu girman gaske, don haka nake son tunasar da kaina da \yan uwa na dangane da wasu daga cikin hakkokin marayu a musulunci, ina mai neman taimakon Allah bisa hakan.

DOMIN ME ZAMUYI MAGANA AKAN MARAYU ?

domin idan maraya ya samu hakkinsa na tarbiyya mai kyau da ingantacciyar rayuwa to hakan yanada tasiri mai girman gaske a cikin al-umma, idan kuwa aka wulakanta maraya ya tashi cikin rayuwa ta tsanani mara kyau to lallai zai iya zama hadari a cikin al-umma. don haka Al-qur'ani mai girma ya bada cikakkiyar wasiyya da kulawa ga marayu, ta hanyar kula da tarbiyyarsa, mu-amalarsa, da kiyaye dukiyarsa, kar kuma a kuskura ayi masa wani abunda ba alkhairi ba.haka nan sunnah tazo domin ta karfafi wannan abin da yazo a Qur'ani ta kuma kara fito da abin fili.[1]

" MA'ANAR MARAYA "

kalmar " اليتيم " maraya a larabci tana nufin kadaita, kuma ,araici a cikin mutane yana kasancewa ne ta bangaren uba, a cikin dabbobi kuma ta bangaren uwa. don haka duk wanda ya rasa uwa kadai a mutane ba maraya bane....." wannan bayanin yazo a littafin lisanul-arab v:6 p:494 da kuma littafin mukhtarus-sihah p:741. maraya kuwa a shari'ah shine : karamin yaro ko yarinyarda mahaifinsu ya rasu basu kai minzalin balaga ba. domin manzon Allah yace: " babu maraici bayan mutum ya fara mafarki balaga. wannan hadisi abu dawud ne ya rawaito shi daga Aliyu bin abiy dalib Allah ya kara masa yarda.[2]

MA'ANAR KYAUTATAWA MARAYA :

Shine kula dashi da bashi tarbiyya ta addini, da kula da al-amuransa ta bangaren ci da sha da sutura da magani yayin rashin lafiy da karatunsa da kula da dukiyarsa tare da juya ta idan yana da ita.idan kuwa bashi da ita sai ayi masa domin neman yardar Allah. {Al-kaba'ir p:72 }

YADDA ALLAH YA HADA KADAITA SHI DA KYAUTATAWA MARAYA:

Allah madaukaki yana fada a cikin Al-qur'ani : " ku bautawa Allah kar kuyi tarayya dashi da komai, haka nan iyaye a kyautata musu, da makusanta [ dangi ], da kuma marayu..." { suratul-Nisa'i V:36}

KYAUTATAWA MARAYU YANA CIKIN MANYAN AYYUKAN DA'A.

Allah mai girma yana cewa: " suna tambayarka dangane da marayu, kace kyautata musu alkhairi ne,idan kuna cakuduwa dasu { wajen abinci } to 'yan uwanku ne, kuma Allah yana sanin mai batawa daga mai kyautatawa, kuma idan Allah yaga dama daya tsananta muku, lallai Allah mabuwayine mai hikima" { suratul-bakara V:220 } Abu dawud ya rawaito hadisi daga dan Abbas Allah ya kara masa yarda yace: lokacinda Allah ya saukar da ayar da take cewa : " karku kusanci dukiyar maraya, sai da abinda yake mafi alkhairi" da kuma ayar da take cewa : " lallai wadanda suke cin dukiyar marayu bisa zalunci......" sai wadanda suke rike da marayu suka tafi suka raba abincinsu dana marayun suka raba abin shansu dana marayun, harya zamto abincinsa zaiyi saura har sai dai marayan yaci abinsa koya lalace. sai hakan yayi tsanani akansu, sai suka gayawa manzon Allah alaihis-salatu was-salam hakan, sai Allah ya saukar da fadinsa : " suna tambayarka dangane da maraya.." sai sahabbai suka dawo suna hada abincinsu dana marayu, abin shansu da nasu.

Manzarta[gyara masomin]

Kulawar Mahaifi ga ƴa ƴansa[gyara masomin]

Ƙagaggen labari !

Ta tambayi Mahaifinta kuɗi Naira dubu biyar, nan da nan sai ya shiga yi mata tambayoyi akan dalilin ta na buƙatar kuɗin, a ran ta sai ta ke jin cewa to don me ma za'a dinga bincikar ta don kawai ta buƙaci only 5k? Amma duk da cewar ba wani kwakkwaran dalili ta bayar ba, atake uban yayi mata alƙawalin zai ba ta kuɗin da safe kafin ya fita wajen aiki.

Bawan Allah! Haka mahaifin nan nata ya kwana ko barcin kirki bai iya ba, domin yana ta nazarin dubu biyarɗin da zai ba ta alhalin baki ɗaya kuɗin da suka rage mashi dubu hud'u da dari biyar (4500) ne.

Da gari ya waye sai ya kira ta ɗakinsa ya ɗauko dubu hud'u ya miƙo mata maimakon dubu biyar da ta buƙata. Ganin anbata dubu hud'un ya sa fuskarta ta sauya, cikin ɗacin rai tayi godiya bayan ta gama ƙorafin 'ai kuɗin ba su cika ba!' haka ta fita daga ɗakin tana guna guni.

A gefe d'aya, Mahaifiyar ta ba tare da ta ce komai ba ita ma ta fita, jim kaɗan ta iske ta a ɗakinta, ta miƙa mata dubu biyu da ta ciro daga cikin kuɗinta. Cikin lallashi take ce mata "Rabu da Babanki kin ji Babyna. Karɓi wannan dubu biyu ɗin ki cika kuɗin da su!"

Farin ciki mara misaltuwa ya baibaye ta nan take ta rungume uwar tana murna "I love you very much Mummy!" Cikin hanzari kuma sai ta ɗauki wayarta, tabi duk shafukan ta na sada zumunta tana rubuta.  " I love my Mother. She's the best Mum in the world!❤

A dai dai wannan lokacin sam ta manta da tsohonta, wanda ya fita da 500 kacal a aljihunsa don kawai ya faranta ran ta.

Allah Sarki! Haka ɗabi'r Mahaifi ta ke. A lokuta da dama ya kan sadaukar da farin cikinsa kacokam don faranta rayuwar iyalinshi, ba kuma tare da ya bari sun fahimci hakan ba saboda Mazantaka!

Yi ƙoƙari ka kayawaita yabawa, akan irin sadaukarwar da Mahaifi ya yi a rayuwarka, domin da ba don ita ba yanzu da ba'a san a wanne irin hali ka ke ba!

Haƙiƙa Mahaifi garkuwa ne! Ina yaba ma Uwaye maza. Ku ma ya cancanta ku yaba wa naku!

  1. Na_Isar!🤷🏽‍♂ Bello Yusha'u (talk) 23:39, 16 ga Janairu, 2023 (UTC)[Mai da]

Sunayen Nana Faɗima Alaihassalatu Wassalam[gyara masomin]

GA KADAN DAKA CIKIN SUNAYEN MAULATY SAYYIDA NANA FADIMATUZ-ZAHRA'U(AS) 1 *_Abida_* 2 *Aliema* 3 *Arradiyya* 4 *Alawiyya* 5 *Atika* 6 *Azeema* 7 *Azeeza* 8 *Amira* 9 *Aliyya* 10 *Batula* 11 *Baki'a* 12 *Baraka* 13 *Bintul rasul* 14 *Bidi'atu mustapha* 15 *Dayyiba* 16 *Dahira* 17 *Fatima* 18 *Farida* 19 *Fa'ika* 20 *Fa'iza* 21 *Fauziyya* 22 *Fadila* 23 *Fasiha* 24 *Husna* 25 *Hafiza* 26 *Halima* 27 *Hani'a* 28 *Hamida* 29 *Harira* 30 *Hakima* 31 *Hauraul insiyya* 32 *Iklima* 33 *Jamila* 34 *Kausara* 35 *Kuratu ainul rasul* 36 *Khairiyya* 37 *Latifa* 38 *Munira* 39 *Muhaddasa* 40 *Mardiyya* 41 *Makiya* 42 *Madaniyya* 43 *Mazluma* 44 *Mu'umina* 45 *Mubaraka* 46 *Muddahara* 47 *Mukarrima* 48 *Maimuna* 49 *Ma'arufa* 50 *Mashkura* 51 *Muhsina* 52 *Mansura* 53 *Mujahida* 54 *Magsuba* 55 *Makhoura* 56 *Mubashshira* 57 *Nuriyya* 58 *Nabawiyya* 59 *Nakiya* 60 *Nabila* 61 *Najma* 62 *Na'ima* 63 *Nafisa* 64 *Qamariyya* 65 *Qayyuma* 66 *Radiya* 67 *Rahima* 68 *Ra'ufa* 69 *Rafi'a* 70 *Rahina* 71 *Rashida* 72 *Sajida* 73 *Siddika* 74 *Sabira* 75 *Shahida* 76 *Shafi'a* 77 * Salsabila 78 *Sharifa* 79 *Safina* 80 *Salima* 81 *Saliha* 82 *Safwa* 83 *Sayyidatul nisa'il alamin* 84 *Tuhfatul fiddausi* 85 *Takiyya* 86 *Ummul khairi* 87 *Ummul Azhar* 88 *Ummu Abiha* 89 *Ummu aimana* 90 *Wasila* 91 *Walida* 92 *yasira* 93 *Zakiyya* 94 *Zahida* 95 *Zakira* 96 *zuhuriyya* 97 *zahara* 98 *Zunnura* 99* zam-zamiya 100* zaliha

Dan kaunarka/ki da Nana fadima as. Ku turawa yan masoya sayyada as... Suma Bello Yusha'u (talk) 23:44, 16 ga Janairu, 2023 (UTC)[Mai da]

A.S Bello Yusha'u (talk) 23:46, 16 ga Janairu, 2023 (UTC)[Mai da]

Shiru ![gyara masomin]

SHIRU...

Kar kuyi tunanin bamu sani ba shi yasa muka bar magana, a'a, bari dai saƙo muke isarwa da yaren da kalmomin mu suka kasa gamsar da waɗanda muke magana dasu. Akwai banbanci sosai tsakanin "SHIRU" da "RASHIN YIN MAGANA" Akwai abubuwa da magana bata iya isarda haƙiƙanin bayanin su, amma SHIRU sai kaga ya tattaro bayanin komai.

"SHIRU" yare ne mai tsada da ba kowa ne yake fahimtar sa ba sai wasu keɓantattun mutane da suka ɗanɗana kuma suka kwankwaɗi zaƙin zumar.

SHIRU fage ne da babu Mai kewayawa aciki sai ma'abota ƙwaƙwalwa da zurfin tunani.

Masu Hikima Suna Cewa....

"Mutum shekara biyu (2) kaɗai yake buƙata bayan an haife shi domin ya koyi magana, Amma zai shafe shekara 50 bai fahimci ma'ana da fa'idar dake cikin tsawaita "SHIRU" ba"

Mu SHIRU Yare ne a wajen mu, kuma Shine Kaɗai yaren da muke jin daɗinsa fiye da sauran yaruka da harshen mu yake furtawa, Shiru siffar mu ce, kuma shine rabin shu'urin mu (Feeling) 😌

A yaren "SHIRU" muka koyi Ƙarancin sharhi da fayyace komai ga mutanen dake tare damu, saboda muna da yaƙinin masoyan mu su ne kaɗai masu fahimtar maganar mu koda muna cikin yanayin shiru.

Shi "SHIRU" Aboki ne da baya ƙarya kuma baya ha'inci, shiyasa duk maganar da ta fito bayan zama dashi sai ka jita cike da gaskiya.

Yana da kyau Kusani.. "SHIRU" baya Nufin tsoron yin martani ga abokin muhawara, barima shine martani mai cike da ma'ana ga ma'abota hankali. Haƙiƙa a yanzu mun gwanance a "Shiru" wajen duk mai muna wauta, kuma hakan baya nufin yarda da abunda yake faɗa, a'a amsa ce kawai da muke nuna musu mun gaji da yi masu bayani dan su fahimta.

Ayi KURUM ayi SHIRU 👌🏽

  1. Na_isar 🤌 Bello Yusha'u (talk) 23:50, 16 ga Janairu, 2023 (UTC)[Mai da]
  1. https://aminiya.dailytrust.com/abubuwa-bakwai-masu-halakarwa-8
  2. http://munbarin-musulunci.blogspot.com/2013/03/abubuwa-bakwai-masu-halakarwacin.html?m=1