User:Jeeddarh

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

AUNTY NIKE SCHOOLS KATSINA

An kirkiri makarantar ne a shekara ta dubu biyu da goma, ashirin da bakwai ga watan satumba da dalibai kwara hudu kacal masu suna; Renni Edwards, Florence Alake Mathins, Ayomide Afolabi Oyeyemi, da kuma Ifeanyi Emmanuel.

Makarantar ta fara ne a tsohon ginin Adeleke daura da bankin ECO akan titin IBB kofar kaura a cikin jahar katsina a inda aka fara da bangaren firamari da naziri.

A cikin shekara daya yawan dalibai suka karu zuwa arba'in da biyar. Makarantar ta cigaba da samun cigaba a inda yanzun daliban su sunkai dari shidda tare da malamai da sukai sittin.

I zuwa yanzun makarantar ta samu cigaba sosai da taimakon ubangiji da kuma ma'aikata masu hazaqa da kuma mutanen da suka sadukar da lokacin su da dukiyar su kamar su mariganyi Alhaji Raji, Alhaji sabi'u Ruma da kuma Alhaji Usman Nadada.

A kowace shekara, makarantar tana yaye dalibai masu hazaqa da kokari.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]