User:M-Mustapha

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Animated-Flag-Nigeria.gif

"Ba zaka taɓa yin nadamar kyautatawa ba!"

Covid19 protective measures.gif


Shawarwari[gyara sashe | Gyara masomin]

Ba kowace kalma bace zaka samu a kowane yare[gyara sashe | Gyara masomin]

Me yasa nake barin references na turanci a rubutu na?[gyara sashe | Gyara masomin]

Ni nasan cewa mutum nason abunda yakeso kuma yakan ƙi abunda baya so, hakane yasa wani zai iya yin rubutu akan wani abu, waɗanɗa basu dace ba, koda ƙarya ne, mutuƙar baya son wannan abu, to zai kushe shi, amma a abunda yakeso, to zakaga ya kuranta abun koda ko ba haka bane, kuma bazai taɓa faɗin asalin yadda wannan abu yake ba. Mungode da cewar Wikipedia bata amince da yin haka ba. Ko menene zakayi rubutu akai, to sai ka sanya nassi, wato asalin inda ka samo maganar (bayanai) da kake rubutuwa, kuma nassin yakasance ingantacce daga mashahurin kafa, bawai daga kafafen shashi ka faɗi ba, domin hakane kawai zai ba mai karatu damar da idan yana tantama yabi wannan nassin domin yaƙara nazari da bincike akan abunda yakaranta daga shafin wikipedia. Wannan ne yasa Wikipedia tazama mafi kyawon wuri da zaka sami bayanai akan abu da inganci, fiye da duk sauran kafafe dake tattara ilimomi na bayanai da akekira da insakulofidiya. Kuma dole amatsayinka na marubuci dole ka zama mai faɗin gaskiya, shi yasa aka ce, a kawai inda zaka samo bayanai shine daga manya-manyan kafafe shahararru kuma ingantattu, bawai daga kafafen tallace-tallace ba, ko na kasuwanci da dai sauransu, wadanda kawai sunfi rinjaya ne akan kurantawa ko kushewa. Shiyasa duk kasidar da zan fassara ko rubutawa nake kokarin aje asalin nassoshin kasidar, dukda cewa ba'a Hausa suke ba, amma sanya su shine zai ba wa mai-karatu kwarin-gwiwa da cewar ga daga inda asalin bayanan suke, kuma har in bai gamsu da wani abu ba, zai iya yin nazari da kansa, kamar yadda wanda ya rubuta asalin kasidar yayi.

Fassara[gyara sashe | Gyara masomin]

Shin kana yin Fassara daga wasu shafukan Wiki zuwa Hausa? Ko kana yin Fassara a wani wurin daban? Shin ka taba cin karo da matsala na wata kalma da baka iya bata ma'ana ba? Ko kuma kaci karon sabbin kalmomi na zamani? Wadannan tambayoyi duk zaka magance su a kankanin lokaci, idan Kalmar sabuwa ce, gashi kuma babu ita ko fassaran ta a harshen Hausa, to kada kace dole sai ka samo wata kalma ka Fassara ta, domin yin hakan zai sa ka bata lokacin ka, kuma sannan kayi mata fassarar da ba haka take nufi ba; kasani acikin kowace harshe, an yarda da ayi aron Kalma, idan ka duba harshen turanci, yawancin kalmomin kimiyyar su, ba daga asalin turanci suke ba, zaka ga aro su akayi daga Latin, Girka(Greek) da sauransu, haka idan ka duba wasu yaruka, suma haka zaka gani. Shi yasa idan har kana fassara ka gamu da kalma sabuwa, ko kalmar wata sana'a, kawai ka dauki sabuwar kalmar acikin Fassarar ka, wato kada ka fassara ta, yi aronta wurin Santa ta cikin fassarar ka, misali, kalma kamar imel (Email), kaga yanayin rubutun kawai aka chanja, kuma ita mutane sukafi amfani da ita, amma idan akace maka kifdau kaga da wahala ace kasan dashi, wanda fassarar da wani Farfesa yawa Kalmar Email kenan.