User:Mustapha Gambo

Page contents not supported in other languages.
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Mustapha Gambo

Sunana Mustapha Gambo Muhd.

An haife ni a Unguwar Gama (A) cikin Yankin Karamar Hukumar Nassarawa da ke Jihar Kano, Najeriya.

Na halarci Makarantar Firamare ta Gama Tudu da Makarantar Sakandiren Koyar da Kasuwanci dake hanyar Filin Jirgin Sama a Kano.

Daga nan na halarci Kwalejin Share Fagen Shiga Jami,a (CAS KANO) na samu Gurbin Shiga Jamiar Bayero dake Kano a Tsangayar Koyar da Aikin Jarida (Mass Communication)

Na yi Hidimar Kasa a Jihar Adamawa.

Na yi aiki a Kamfanin Fulawa na Dangote a matsayin Jami'in Kula da  korafin Hulda da masu Kamfanin.

Daga nan na samu aiki a Gidan Rediyon Najeriya a matsayin Mai dauko rahoto inda a yanzu haka nakai matakin Babban Mai dauko Rahoto( Senior Reporter).

Bayan aikin dauko rahoto Kuma na zamanto Editan labarai da karantawar Labaran Hausa da Turanci.

A yanzu haka nine Shugaban Kungiyar Yan Jaridu NUJ reshen Gidan Rediyon Najeriya Pyramid FM Kano inda aka zabe ni karo biyu a jere.

Sannan nine Sakataren Kungiyar Yan Jaridu Masu dauko rahoto daga kotuna da Yansanda na Jihar Kano.

Ina da Sha,awar Kallon kwallon kafa, Tafiye- Tafiye da Karance-Karance.