Jump to content

User:Salihu Aliyu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Game da Ni

Barka da zuwa shafi na! Sunana Salihu Aliyu Alhaji. Ni mutum ne mai sauƙin kai kuma mai son hulɗa cikin natsuwa. Ina son rubuce-rubuce da karanta littattafan soyayya. Na karanta fannin sashen Sadarwa a Kwalejin Kimiyya ta Kaduna (Kadply). Ina da sha’awar aikin jarida, kuma ni ɗan asalin Hausa-Fulani ne. Launin da na fi so shi ne kore, Nafi son lokacin damina. Ina alfahari da kasancewata editan Wikipedia! Ina alfahari da kasancewata ɗan Najeriya! Ina alfahari da kasancewata ɗan Afirka!

Ina son yin abubuwa masu inganci, kuma bana damuwa da yin abubuwa masu yawa, matuƙar suna da ma’ana — ba wai taron yu-yu ba marasa amfani. Ina son gaskiya da amana, kuma ba zan taɓa jin kunya ba game da hakan, ko a ina, a kowane lokaci, a kowane irin hali. Ina matuƙar son mutane masu gaskiya da amana. Ni mutum ne mai sarin tausayawa, kuma ina jin tausayin duk wani mutum da yake cikin wani yanayi mara daɗi.

Salihu Aliyu Alhaji
Harsunan edita
ha-5 Wannan edita ya karanci Hausa sosai.
en-3 This user has advanced knowledge of English.
ar-3 هذا المستخدم لديه معرفة متقدمة بالعربية.
ff-3 This user has advanced knowledge of Fulfulde.
Editoci da yarensu

Contact:saliyualhaji@gmail.com