Victoria Island (Najeriya)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Victoria Island daya ne daga cikin cibiyoyin hada-hadar banki da kasuwanci a Najeriya, waanda ya zama hedikwatar mafi yawan manyan bankunan Najeriya da kuma kamfanoni na kasa da kasa.[1] Tsibirin Victoria na daya daga cikin gundumomi a Jihar Lagos kuma tana iyaka da tekun Atlantika ta bangaren kudu, tafkin Legas a bangaren yamma da kuma Five Cowrie Creek daga arewa.[2]

Bayani[gyara sashe | gyara masomin]

Victoria island na daya daga cikin wurare mafi keɓanta da tsadar rayuwa a Najeriya[ana buƙatar hujja], ya shahara tsakanin ƴan ƙasar waje da ma'aikatan kamfanoni na ƙasa da ƙasa.

Victoria Island tana da ɗimbin gidajen cin abinci, manyan kantuna, otal-otal, mashaya, Gidan Rawa, gidajen sinima da sauran ababen More rayuwa na masu Hannu da Shuni. Tsibirin Victoria yana tsakanin Lekki da tsibirin Legas, Wuri ne na masu hannu da shuni. Ana rade-radin cewa gidan manyan mutane ne kuma yana cikin karamar hukumar Eti-Osa a jihar Legas. Gidan sarautar Oniru sune suka mallaki kaso mai yawa na Victoria island har sai da hukumar raya kasa ta Legas ta biya fam 250,000 a matsayin diyya ga filin da kuma karin fam 150,000 a matsayin diyya na wuraren ibadar da aka lalata a 1948. Daga karshe an tilasta wa mazauna garin su kaura zuwa kauyen Maroko.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]