Jump to content

Wasika

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
wasika
literary genre (en) Fassara da literary form (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na document (en) Fassara, personal testimonial (en) Fassara, written work (en) Fassara da mail item (en) Fassara
Masana'anta mail (en) Fassara
Amfani sadarwa
Has characteristic (en) Fassara message (en) Fassara
wasika
wasika

Wasiƙa rubutaccen saƙo ko bugagge wanda mafi yawancin lokuta akan saka ta cikin ambulan sannan a aikawa wani mutum, ƙungiya, hukuma da sauransu.

Rabe-Raben Wasiƙa

[gyara sashe | gyara masomin]

Wasiƙa ta kasu zuwa rukunnai guda uku kamar haka: 1. Fomal leta: a Turance ana kiranta “formal letter” ko kuma “Official letter”. Kamar yadda sunanta na biyu ya ke, wasiƙa ce da ake rubuta ta akan abin da ya shafi harkar ofis. Takan iya zama tsakanin mutum da mutum wanda ɗaya daga cikinsu kan kasance ofisa ne, ko kuma tsakanin ofis da ofis. Misali, Ado ya rubuta zuwa ga Inuwa, wanda shi kuma Inuwa yana riƙe da wani ofis. Ko kuma misali a ce gwamna ya rubutawa wani gwamnan, ko kuma wata jahar ta rubutawa wata jahar misali, Jigawa ta rubutawa Kano. Wajen rubuta fomal leta ana rubuta ta da adireshi biyu. Adireshin mai turawa (wanda ya rubuta wasiƙar) daga saman takarda a gefen dama, da kuma adireshin wanda aka turawa daga ƙasa da wancan adireshin na farko a ɓarin hagu. 2. Infomal leta (Informal Letter): Wasiƙa ce ta dangantaka. Ana rubuta wannan wasiƙa zuwa ga abokai, ‘yan’uwa, iyaye, da sauran makamantansu. Wasiƙa ce da ake rubuta ta ga wani mutum da ka sani. Wajen rubuta wannan wasiƙa adireshi ɗaya ake rubutawa daga sama a ɓarin dama, wanda shi ne adireshin mai turawa (wanda ya rubuta wasiƙar). 3. Semi-fomal leta (Semi-formal letter): Ita wannan wasiƙa ce da ke rigar tsakanin, it aba cikakkiyar fomal leta ba sannan kuma ita ba informal leta ba. Ana rubuta wannan wasiƙa zuwa ga abokan iyaye, malaman makaranta, malaminka na addini, shugaban makarantarka (principal ko waninasa), sai dai idan za ka aika zuwa ga shugaban wata makarantar da ba taka ba, to a nan fomal leta za ka rubuta.

Ɓangarorin Wasiƙa

[gyara sashe | gyara masomin]

Wasiƙa tana da ɓangarori kamar haka: 1. Salutation: Ita ce gaisuwa. Akwai bambanci tsakanin yadda ake rubuta gaisuwar fomal leta da kuma ta saunar biyun. Gaisuwar fomal leta: Yawancin gaisuwar fomal leta takan zamo “Dear Sir” ko kuma “Dear Madam”. Sannan ita kuma semi-fomal leta gaisuwarta takan zama ɗaya daga cikin waɗannan gaishe-g