We, Students!

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
We, Students!
Asali
Characteristics
External links

We, Students! ( French: Nous, étudiants) fim ne da a ka shirya shi a shekarar 2022 na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wanda Rafiki Fariala ya rubuta kuma ya ba da umarni kan fasalin fim ɗinsa na farko.[1] Fim ɗin ya nuna tsantsar gaskiya game da yadda ake renon ɗalibai a Jami'ar Bangui a cikin batutuwa daban-daban kamar cin zarafi na jima'i, mummunan yanayin rayuwa a cikin harabar jami'ar da kuma gaskiyar cewa dole ne a jure wa manyan ayyukan rashawa da farfesoshi suke yi. Fim ɗin ya zayyana da kuma nuna yadda ɗan fim ɗin kansa da abokansa na jami'ar Bangui ke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, kuma sun yi watsi da tunanin yadda makomarsu za ta kasance a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a nan gaba.[2][3] An nuna fim ɗin a sashen Panorama a bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa na Berlin karo na 72 kuma ya zama fim na farko da aka taɓa yi daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da aka fara nunawa a bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa na Berlin.[4][5][6] A cewar rahoton The Africa , an sanya shi cikin manyan fina-finan Afirka goma da suka fi fice a shekarar 2022. [7]

'Yan wasa[gyara sashe | gyara masomin]

  • Rafiki Fariala a matsayin kansa
  • Nestor Ngbandi Ngouyou
  • Haruna Koyasoukpengo
  • Benjamin Kongo Sombot
  • Rafiki Fariala

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Nous, étudiants! | Viennale". www.viennale.at (in Turanci). Retrieved 2022-12-28.
  2. "ICA | UK PREMIERE We, Students! (Nous, étudiants!) + Q&A". www.ica.art. Retrieved 2022-12-28.
  3. "We, Students! (Nous, étudiants !)". Cineuropa - the best of european cinema (in Turanci). Retrieved 2022-12-28.
  4. "Panorama 2022: The First 13 Titles Confirmed". Berlinale. 15 December 2021. Retrieved 2022-12-28.
  5. Grater, Tom (18 January 2022). "Berlin Film Festival Finalizes Panorama Line-Up; Unveils Series Market & Co-Pro Series Selections". Deadline (in Turanci). Retrieved 2022-12-28.
  6. "Nous, étudiants ! | We, Students! - Panorama Dokumente 2022". www.berlinale.de (in Turanci). Retrieved 2022-12-28.
  7. https://www.theafricareport.com/269247/drc-nigeria-south-africa-the-10-most-notable-african-films-of-2022/