Jump to content

Wesoła Lwowska Fala

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Wesoła Lwowska Fala
radio program (en) Fassara

Wesoła Lwowska Fala (Yaren mutanen Poland na Lwów's Merry Wave ) shiri ne na gidan Rediyon Poland Lwow wanda ake gudarwa a duk mako, Gidan Rediyon Poland ke watsa shi a kowace ranar Lahadi. Galibi dai shirin ya ƙunshi ‘yan kade-kade, zane-zane da raha, yana daya daga cikin shirye-shiryen gidan rediyon mafi shahara a Poland a tsakanin zamanin yakin duniya. An fara shirin a 1933, ya kasance a shirin yanar gizo har zuwa mamayewar Poland na 1939.

Kamar yadda shirin yake gudana na tsawon yini guda, wanda daya daga cikin reshen gidan Rediyon Poland ya shirya, maimakon ofishin babban edita, ya kasance sabon abu, asalin shirin ana watsa shi ne kusan a kyauta daga 'yan jaridu da ‘yan wasan barkwanci. Zuwa wani dan lokaci shirin ya zamo daya daga cikin sheirye-shiryen gidan rediyon Poland mafi shahara, wanda sananne ne a duk fadin ƙasa.

  • Tashoshin rediyo a cikin Poland

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]