Wikipedia:Gasar WPWA Hausa
Wiki Sound Audio Speaks Campaign gangami ne na Wikimedia yana mai da hankali kan babbar gudummawar Fayilolin Sauti waɗanda suka cancanci encyclopedic don sauƙin raba ilimi kyauta. An tsara wannan kamfen don samar da fayilolin odiyo masu ilimi kyauta na harsuna daban-daban zuwa cikin Wikimedia Commons da kuma haɗa su cikin sauran aiyukan Wikimedia na Harshe daban-daban, da kuma ƙara yawan fayilolin sauti a cikin Wikimedia Commons da yin amfani da waɗannan fayilolin a cikin ayyukan Wikimedia daban-daban musamman ma ayyukan harshe kamar (Wikipedias da Wikitionaries). Kusan duk shafukan Wikimedia suna buƙatar fayilolin sauti, don haka aka tsara wannan shirin domin samun ainihin masu jin kowanne harshen su samar da sautuka a cikin harsunan su a Wikimedia Commons.
Hausa WPWA Contest wannan gasar zata mai da hankali ne akan daura sautuka (sounds) akan shafuka ko muƙaloli na Wikicommons, wikitionary da kuma Wikipedia.
Dawaya daga cikin shafuka ko muƙalai na Wikipedia da na wikitionary suna bukatar a daura musu sautuka (sounds) domin mai karatu yaji yadda ake furta wasu kalmomin.
Musamman idan muka dauki wikitionary zamuga cewar yana dauke da kalmomi ne tare da ma'anoninsu kana mutane da dama suna yin karance-karance dama yin research (wato bincike) na wasu kalmomin da aka daura su a Hausa wikitionary amman wajen furta wasu kalmomin akan samu matsala daga gare su hakan yasa Wikimedia Foundation suka ga cewar yadace a daura sautuka (sounds) a wadannan muƙalolin domin masu karantawa suna saurara suji yadda ake furta wadannan kalmomin cikin Harshen Hausa. Wannan tasa aka sanya wannan gasar ta WPWA (wato WikiPages Wanted Audio). Domin karin bayani zaku iya ziyartar Babban shafin gasar a Meta
Manufar Wannan Gasa
[gyara masomin]- Domin Wikimedians su sami ƙwarewa da fasahar loda fayilolin odiyo zuwa Wikimedia Commons, wikitionary da kuma Wikipedia.
- Don cimma burin loda fayilolin sauti guda 1,000,000,000 kafin ƙarshen shekarar 2030 a cikin harsuna daban-daban.
- Don samun adadi mai yawa na editoci da zasu ba da gudummawa na loda fayilolin sauti a wiki commons, wikitionary da Wikipedia.
Yadda ake shiga Gasar
[gyara masomin]- Shiga Ko Kirkiri sabon asusu a Wikipedia.
- Yi rajista a kan Dashboard ɗin Hausa WPWA Contest
- Yi rajista a sashin Participants a wannan shafin.
Za a fara wannan gasar daga ranar 2023 Zuwa 2023.
Latsa wannan link din domin shiga group na WhatsApp WhatsApp group
Makalolin da Ake buƙata
Wadannan sune bangarori (Wikis) da ake buƙatar a daura sautuka (sounds) a muƙalolin su:
Participants
[gyara masomin]Sanya Username dinka a ƙasa: