WP:Hausa Wikipedia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Wikipedia:
Black W for promotion.png

Mukaddiman Wikipedia: Wikipedia ta kasance Insakulofidiya ce ta kyauta, kundi ce na saka bayanan ilimi kyauta, domin bayar da ilimi lakadan ga al'umar duniya gabaki daya, kowa nada cikakkiysr dama da kuma ikon bada gudummawar sa domin girke ilimi da kuma yaɗa ilimin kyauta ga duniya, kuma kowa nada cikakken ikon amfani da kayan da'aka saka a Wikipedia kyauta a karkashin lasisi daban daban, kaman amfani da rubutun ta, hoto da a'aka saka, bidiyo da sauran fayal, kowa zai iya amfani da hajan Wikipedia ya samu ilimi, ko zai iya amfani da ita ta kowace fuska a matakin amfani mai kama da lasisin da'aka wanzar da fayel din, mutane ne ke taimakama Wikipedia ta hanyar saka bayanai kyauta, ko bada dukiya domin taimakon Wikipedia, ko isar da sakon ilimin kundin Wikipedia zuwa ga wasu ɗaukacin mutane, mutane editoci ne suke gudanar da aikace-aikacen gyara Wikipedia a bangarorin mataki daban-daban kyauta, ta hanyan saka bayanan ilimi, da kuma gyara bayanan da aka saka dan inganci da nagarta, sannan mutane editoci ne ke goge bayagurbin bayanai na karya, zagi, ƙazafi da tallace-tallace, a jimlatance, Wikipedia an gina ta ne akan Manufofin Wikipedia guda biyar, sannan tana samun tallafi ne da kuma gudanarwa daga waɗanda suka gina ta, wato Wikimedia Foundation, Dukkan abun da aka rubuta a Wikipedia yana karkashin lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike License, wacce kowa zai iya amfani da ita kai tsaye, da kuma sauran lasisin amfani masu ka'idojin amfani akan ra'ayin masu wanzar da su.

Tango style Wikipedia Selection Icon.svg

Wiki: A Wikipedia akwai yaruka daban-daban, kowanne yare suna rubuta shafukan sune da yaran su, saboda haka waɗannan yarukan sune ake cema Wiki, akwai ƙananan Wiki masu muƙaloli Ƙadan, sannan akwai manyan Wiki masu muƙaloli dayawa, akwai English Wikipedia, Arabic Wikipedia, Yoroba Wikipedia, Igbo Wikipedia, Hausa Wikipedia dadai sauran su. kowanne a cikin waɗannan ana kiran ta da Wiki. Lafazin WikiPedia an samo shi ne daga kalmar Insakolofidiya, in aka ce Insakolopedia ana nufin jadawalin kundin tattara ilimi a jerin tsari mai kyau, A dalilin haka ne aka yi amfani da kalmomi guda biyu Wiki da Pedia, In aka ce Wiki yare kenan, pedia kuma kundi, sai aka hada kalmomin suka bada Wikipedia.

Ƴan uwan Wikipedia: Wikipedia tana da yan uwa guda Goma sha biyu waɗanda suke aiki hannu da hannu a sargafe dan juna, domin taimaka ma Wikipedia gaba daya, kowanne ɗan uwa daga cikin guda Goma sha biyu ɗinnan, yana da aikin da yake yi dan gina Wikipedia, waɗannan yan uwan sune kamar haka:

A sani cewa Ƴan uwan Wikipedia ba Wikipedia bane, shiyasa ake kiran su da Wikimedia sister project,amman Ƴan uwa Wikipedia ne, amman ita Wikipedia akwai ta a yarika daban daban. an kira su da ƴan uwan Wikipedia ne saboda domin Wikipedia aka ƘirƘire su, kuma suna taimaka ma Wikipedia ne Ƙadai domin ci gabanta.

1 - Ƴan uwan Wikipedia

Commons-logo-en.svg

Wikimedia Commons

Faifan saka fayels
|Hoto| |Bidiyo| |Sauti|


Ɗan uwan Wikipedia
Wikipedia:
Commons-logo-en.svg
Wikimedia Commons: Kundin saka fayel na hoto, bidiyo da kuma Sauti.
Commons Wikimedia ta kasance kundi tattara fayel, na Hoto, Bidiyo da kuma sauti, mutane editoci ne suke saka fayel din a cikin faifan kundin, a Commons ne ake girke dukkannin fayel na bangarori daban-daban, kuma daga commons ne Wikipedia ke samun fayel dan amfani a muƙaloli (shafuka), kowanne fayel dake Commons mutane ne suke bada shi kyauta a kan lasisin CC BY-SA 3.0 na amfanin kowa da kowa, ko kuma akan sauran lasisin amfani na fayel. danna wannan mahaɗan domin shiga babban shafin Wikimedia Commons https://commons. zaku iya bayar da hotunan ku kyauta domin cigaban ta, dannan wannan mahaɗan domin saka fayel a Commons Saka fayel a Commons.
WPCube.png
Hoto:Hoto a Wikimedia Commons ana sanya shi ta hanyan Saka fayel a Commons wato ta Wizard upload, shi wannan Wizard upload din hanya ce mai sauƙi da mutum zai bi dan saka hoto, bidiyo ko sauti a Commons, amman dole ne ya zamto cewa hotan naka ne wato (Own-work), ko wani ya bada hotan kyauta wato (Not-own-work) ko kuma hotan yana cikin kayan gandu wato (Public Domain). ka latsa linkin hoto domin samun cikakken bayani akan hoto,
Euforie video generic.pngBidiyo: Bidiyo a Wikimedia Commons ana sanya shi ta hanyan Saka fayel a Commons wato ta Wizard upload, shi wannan Wizard upload din hanya ce mai sauƙi da mutum zai bi dan saka hoto, bidiyo ko sauti a Commons, amman dole ne ya zamto cewa hotan naka ne wato (Own-work), ko wani ya bada hotan kyauta wato (Not-own-work) ko kuma hotan yana cikin kayan gandu wato (Public Domain). ka latsa linkin hoto domin samun cikakken bayani akan hoto,
Talking Wiki Icon.png
Sauti: Hoto a Wikimedia Commons ana sanya shi ta hanyan Saka fayel a Commons wato ta Wizard upload, shi wannan Wizard upload din hanya ce mai sauƙi da mutum zai bi dan saka hoto, bidiyo ko sauti a Commons, amman dole ne ya zamto cewa hotan naka ne wato (Own-work), ko wani ya bada hotan kyauta wato (Not-own-work) ko kuma hotan yana cikin kayan gandu wato (Public Domain). ka latsa linkin hoto domin samun cikakken bayani akan hoto,

2 - Ƴan uwan Wikipedia
WIKIDATA
Kundin tattara bayanai
Ɗan uwan Wikipedia
Wikipedia:
Wikidata: Kundin tattara bayanai
Wikidata kundi ne na tattara taƙaitaccen bayani a kan kowannen muƙala da'ake dashi a ko wanne shafin Wikipedia a sauran yaruka, da kuma alaƙan ta Shafin da hotansa da kuma sunansa, duk wasu muhimman bayanai na asali ana tattarta sune a Wikidata, misali; akwai shafin Muhammadu Buhari a English, Arabic, Dutch, German, Espaniol da dai sauransu, kowanne shafi anyi bayani ne akan Muhammadu Buhari da yaran da aka ambata, to amman akwai abubuwan da iri daya suke a dukkannin yarikan da kuma Wikipedian, kaman shekaran haihuwa, suna, manazarta, hoto, dadai sauransu, to waɗannan abubuwan ne za'a tattara su a Wikidata a basu Code guda daya, code din zai tattara bayanai akan dukkannin sauran shafukan daga kowanna yare, misali: A Wikidata za'a bashi Code da (Q361567), duka shafukan Muhammadu Buhari daga kowanne yare zasu kasance a karkashin wannan Code din ne, shi kuma Code ɗin zai tattara bayanai masu kama da juna dga kowanne shafi, daga kowanne Wiki.

3 - Ƴan uwan Wikipedia
Meta-Wiki
Gidauniyar gudanar da al'amuran Wikipedia da Wikimedia
Yan uwan Wikipedia
Wikipedia:
Meta-wikiL.jpg Meta-Wiki: Gidauniyar gudanar da aikace aikacen Wikipedia da Wikimedia.
Meta gidauniya ce dake samar da ma'amala tsakanin Editocin Wikipedia da kuma sauran Wikimedia masu bada gudummawa a cikin tafiyar da aikace-aikacen manufar furojet na gidauniyar Wikimedia Foundation, a karkashin wannan gidauniyar ne bangarori daban daban suke tattauna akan ci gaban Wikipedia da samar da furojet dan ɗabbaga ta.4 - Ƴan uwan Wikipedia
Wikitionary
Kundin tattara ma'anonin kalmomi
Ɗan uwan Wikipedia
Wikipedia:
Wikitionary: Kundin tattara ma'anonin kalmomi
Kundi ne dake dauke da ma'anonin kalmomi a harshen Hausa, ana bayanin kalma akan gaba gaba, da yanayin furucin kalma,Bude shafin aiki (Akount)


Scale icon green.svg

Shafin aiki: Idan anada bukatar a a yi rejista a Hausa Wikipedia za'a iya yin rejista ta wannan link din Bude shafin aiki (Akount) ko kuma a kalla wannan bidiyon domin sanin yanda ake kirkiran akount kyauta a Wikipedia, ko kuma ta hanyar sauke karamain daftarin karatu wato pdf domin sanin hanyoyin da za'a bi wajen kirkiran akount a Hausa Wikipedia, ko kuma ka sauke Bidiyo koyo domin kallan yanda ake kirkiran akount a Hausa Wikipedia.

Ƙirƙiran muƙala


Encyclopedia icon.svg
Wannan PDF ne dazai taimaka maka wajen koyan yanda ake Ƙirƙiran shafi a Hausa Wikipedia.

Muƙala: Muƙala na nufin shafin dake dauke da bayanai a mahanga ta ilimi, wacce aka rubuta ta a bisa turban gaskiya da ilimi, ana samar da madogaran zance wato manazarta akan duk wani bayani da'ake gudanarwa a cikin muƙaloli, rubuta muƙala na bukatar maida hankali akan iya rubutu, sanin harshe da kuma jera bayanai, dolene kuma ya zamto cewa muƘaloli suna kamanceceniya da juna ta fuskar tsari da kuma yanayin rubutu, domin sanin cikakkiyar hanyan da'ake bi wajen Ƙirkiran Muƙala a dannan wannan link din Yadda ake rubuta muƙala ko kuma ka sauke karamin daftarin karatu a nakura mai ƙwaƘwalwa ko kuma a wayar ka ta hannu, ta hanyar danna wannan hotan dakake gani a gefan dama.
Light bulb icon red.svg


Gamammiyar ka'idojin amfani: Wikipedia na da ka'idojin amfani da kuma gudanar da sauye sauye a Wikipedia, ta yanda zai kasance Wikipedia da sauran yan uwan ta sun kasance farfajiya mai tsafta da kuma kyau, ta hanyar da kowa zai iya saka ilimi a Wikipedia batare da an tsangwame shi ba, ko kuma hantara ba, da kuma samar da wasu ka'idojin da zasu ringa kare hakkokin masu bada gudummawa wato editoci a Wikipedia, hanya ce wacce akeson ya zamana cewar kowa ya samu dama da iko iri daya, kama daga masu bada gudummawa, ma'aikatan Wikimedia Foundation da kuma kwamitin amintattu.


Wikipedian icon.png

Editocin Hausa Wikipedia: A hausa Wikipedia akwai mutane masu taimakawa wajen saka ilimi kyauta, da kuma gudanar da gyare gyare domin yada ilimi kyauta ga duniya.


Blue flat directory icon.svg

Neman taimako: Idan ana bukatar taimako a Wikipedia za'a iya yin amfani da wannan link din domin neman taimakoSmiley icon light.svg
Jigsaw piece yellow 01.svg
Well-wikipedia.svg
Red flat directory icon.svg
Ambox move.svg
Icon-wrench.png
Icon-addlinks.png
Mail.png
Odebranie DA orange.svg
Paid contributions slogan.svg
Structurism icon.svg
No trash in wiki icon.svg
No personal attacks.jpg
RedaktionHund.svg
Hausa Wikimedians User Group Logo.svg
Jigsaw piece yellow 01.svg