Wikipedia:Labarai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Hausa[Gyara masomin]

Gina Sakakken encyclopedia cikin Hausa – saƙo daga ƙungiyar Wikimedia ta Najeriya, bangare na Gidauniyar Wikimedia da ke gudanar da Wikipedia, babban shafin yanar gizon duniya. Ƙungiyar Wikimedia ta Najeriya na gabatar da ‘yantacciyar damar ilimi.

Wikipedia shirin encyclopedia ne wanda Gidauniyar Wikimedia ne ke tallafa masu. Masu sa kai (masu ganin dama) ke rubutawa ba tare da biya ba. Duk wanda ke da halin hawa yanar gizo na iya rubutawa da kuma gyare-gyare ƙasidu a shafin Wikipedia. Tun kafuwarta a shekara ta 2001, Wikipedia ta yi girma zuwa babban shafin yanar gizo, wanda hakan ya jawo ra’ayin miliyoyin baƙi musamman a wata da kuma dubban dumbin mutane wanda ke gyare-gyaren ƙasidu, sabunta su ko surubuta sabbi a kowace rana.

Wikipedia a Hausa (ha.wikipedia.org idan kana amfani da na’ura mai kwakwalwa – wamfuta – ko ha.m.wikipedia.org idan kana amfani da wayar hannu) ta ginu cikin yan shekaru da suka gabata. A Janairu 2019, tana da kasidu dubu uku da ɗari ɗaya da hamsin (3150) kuma kusan mutum arba'in (40) na taimakawa wajen kara ilimi akan encyclopedia din a kowane wata, amma har yanzu shirin ƙarama ce kuma tana bukatar gudummuwarka. Gaggarumar hanya ce ta ba da damar ilimi ga mutane, musamman ga waɗanda basu iya karatun Turanci ba yadda ya kamata.

Idan akwai wani fanni ko fage na musamman, ko ilimin yanayi, ko tarihi, addini, magunguna, ilimin kimiya, gwaninta, girki, noma da kuka sani… ana iya kawo (ko rubutawa) domin karuwa al’ummar duniya. Za ka iya yin rubutu akan muhallinka, kauyenka, jami’arka, kamfaninka, siyasa, wasanai, da dai duk wani abinda ka ga damar yin rubutu a kai, kuma zai amfani al’umma.

Mutane daga kowane ƙabila, matsayin shekaru, ko matsayin ilimi kan iya yin gyara akan kasidu da ke a kan shafin ko su rubuta sabbi, shekaru ba su hana wannan aiki. Idan ka iya Turanci ko Farasanci, za ka iya fassara kasidu daga Wikipediar Turanci da Farasanci zuwa Hausa a akan Wikipediar Hausa.

Mutane sama da miliyan ɗari (100'000'000) na magana da Hausa a Ƙasashe sama da goma (10). Yanar gizo ta musamman, wato Wikipedia cikin Hausa na ba da babban damar fadada ilimi ga miliyoyin mutane. Idan kana ganin zaka iya kawo gudummuwa don wannan aikin, don Allah ka/ki rubuta ha.wikipedia.org idan kana amfani da kamfuta ko ha.m.wikipedia.org idan kana/kina amfani da waya mai yanar gizo. Kana iya zaba kowane kasida ka danna kan “gyara masomi” domin gyara wani kuskure da kuka gani. Ko kuma inganta bayanin. Mun gode da taimakonka/ki!

Wannan saƙo ne daga Ƙungiyar Wikimediar Najeriya, bangare na Gidauniyar Wikimedia da ke gudanar da Wikipedia, babban shafin yanar gizon duniya. Ƙungiyar Wikimedia ta Najeriya na gabatar da ‘yantacciyar damar ilimi.

English[Gyara masomin]

Building a free encyclopedia in Hausa – A message from Wikimedia UG Nigeria, an affiliate of Wikimedia Foundation that run Wikipedia, the world largest online encyclopedia. Wikimedia UG Nigeria promotes access to free knowledge.

Wikipedia is a encyclopedia project supported by the Wikimedia Foundation. It is written by volunteers who write without pay. Anyone with internet access can write and make changes to Wikipedia articles. Since its creation in 2001, Wikipedia has grown rapidly into one of the largest websites, attracting hundreds of millions of uniques visitors monthly and hundreds of thousands of people who make changes to articles or create new ones.

Wikipedia in Hausa (ha.wikipedia.org if you are using a computer or ha.m.wikipedia.org if you are using a smartphone) started a few years ago. As of January 2019, it has 3150 articles, and about 40 people are helping to add knowledge to the encyclopedia every month. It is still a small project and it needs your help. It is a great way to give access to knowledge to many people, especially those who are not able to read English very well.

If you have knowledge in a specific area, be it geography, history, religion, medicine, science, arts, cooking, agriculture... you can bring a stone to the building. You can even write about your neighbourhood, your village, your university, your company, politics, sports, anything. People of all ages, cultures and backgrounds can change existing articles or create new ones. If you speak English or French, you can translate articles from the English and French Wikipedias into Hausa on the Hausa Wikipedia.

Hausa in spoken by more than 100 million people in more than 10 countries. Internet and especially Wikipedia in Hausa give a big opportunity to improve access to knowledge for millions of people. If you think you can bring something to this project, please go to ha.wikipedia.org if you are using a computer or ha.m.wikipedia.org if you are using a smartphone. Just go to any article and click on “edit source”. Thanks for your help!

This a message from Wikimedia UG Nigeria, an affiliate of Wikimedia Foundation that run Wikipedia, the world largest online encyclopedia. Wikimedia UG Nigeria promotes access to free knowledge.