Wikipedia:Rudanin Ra'ayi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Rudanin Raayi ya ƙunshi ba da gudummawa ga Wikipedia game da kanku, dangi, abokai, abokan ciniki, ma'aikata, ko kuɗin ku da sauran alaƙoko wadanda suka shafeku. Duk wata dangantaka ta waje na iya haifar da rudani na ra"ayi. Rudanin ra'ayi kamar bayanine na yanayi, bawai yanke hukunci ba akan ra'ayi, mutunci ko kuma imani. Ana tsanar rudanin Ra'ayi akan Wikipedia sosai. Saboda Yana iya lalata amincin jama'a da kasadar haifar da kunya ga jama'a ga daidaikun mutane da kamfanonin da ake tallatawa. Masu gyara tare da Rudani na son rai, wani lokacin ba su da masaniya akan yadda yake shafar rubutunsu.