William H.J. Rangeley
Appearance
William H.J. Rangeley | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1910 |
Mutuwa | 20 ga Maris, 1958 |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Rhodes Brasenose College (en) |
Sana'a | |
Sana'a | anthropologist (en) |
Kyaututtuka |
gani
|
William HJ Rangeley (1910-1958) jami'i ne a mulkin mallaka na Nyasaland kuma masani kan tarihin baka da kabilanci na mutanen kasar Malawi a yanzu.[1]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]William Rangeley, wanda ɗa ne ga majagaba biyu na farko na Arewacin Rhodesia, Henry Rangeley da Florence (née van Breda), an haife shi a Fort Jameson, (yanzu Chipata, Zambia), a cikin ƙasar Rhodesia ta Arewa a lokacin, ranar 2 ga Yuli 1909. Ya halarci makaranta a Plumtree a Southern Rhodesia, sannan Colejin Diocesan a Rondebosch, wani yanki na Cape Town, a Afirka ta Kudu. Ya halarci Jami'ar Rhodes da ke Grahamstown kuma, a ƙarƙashin Skolashif na Rhodes ya yi karatu a Kwalejin Brasenose, Oxford, daga baya ya sami difloma a Anthropology bayan karatu a lokacin tsawaita hutu.[2][3]