Yadda Ake Turaren Wuta Na Musamman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Turaren wuta ana yin sa ne da itace, domin turara ɗaki, da dukkanin jiki da na tsugunno, da kuma na sutura. Ana zuba shi cikin gaushi (garwashi) ne a kasko. Nan da nan kuwa ka ji ƙamshi ya gauraye ko’ina a cikin gida. Daga cikin Itatuwa da ake turare da su kuwa Sun haɗa da:

Icen Sandal

Icen, Hawi

Icen Gab-Gab

Icen Durot Da dai Sauransu.[1]

Larabawa da kuma mutanen Maiduguri ne suka fi shahara wajen amfani da turaren wuta. Mazansu na taimakawa sosai, su siya wa matansu turare akai-akai. A wajensu tamkar dole ne amfani da turare . Mace ba ta da daraja sai da kasancewa cikin ƙamshi a kodayaushe .[2]

Yadda ake haɗawa[gyara sashe | gyara masomin]

Za a sa icen Hawi a turmi a daddaka shi sama-sama. A sa icen gab-gab shima haka. Sai a juye su cikin mazubi. A dauko ruwan turare Matan Arewa a zuba a kan itatuwa.[3] A juye Soyayyen farce. A zuba Misik. Sai a ɗauko turaruka: Alhaji Abdullahi, da salamalekum, da Sasorabia, da 20 fragrances. Kowanne a buɗe a juye. Sai kuma a dauko madarar turare masu matukar ƙamshi a zuba su. A juya da kyau ko’ina ya samu ya haɗe . A samu mazubi a juye a ciki. Kuma a rufe shi sosai.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]